ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shekaru 6 Bayan Zanga-zangar #EndSARS: Abubuwa 8 Da Suka Girgiza Nijeriya

by Sadiq
4 days ago

Shekaru shida bayan zanga-zangar #EndSARS, ’yan Nijeriya na ci gaba da tunawa da yadda dubban mutane suka yi ƙoƙari wajen neman kawo ƙarshen cin zarafin jama’a da jami’an ’yansanda da kuma rashin kyakkyawan shugabanci.

Zanga-zangar ta fara ne a watan Oktoban 2020, kafin ta bazu zuwa jihohi sama da 20.

Matasa sun buƙaci a yi adalci, a ɗora wa masu laifi alhaki, tare da rushe rundunar ’yansanda ta musamman mai yaƙi da fashi da makami, wato SARS.

ADVERTISEMENT

Ga muhimman abubuwa guda takwas da suka faru a lokacin zanga-zangar:

1. Harbin masu zanga-zanga a Lekki Toll Gate: A ranar 20 ga watan Oktoban 2020, sojoji sun buɗe wa masu zanga-zanga a Lekki Toll Gate da ke Legas wuta, lamarin da ya ja hankalin duniya.

LABARAI MASU NASABA

Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya

Jam’iyyu Da Ƴan Takara Sun Yi Wa INEC Bore Kan Cire Sunayensu Daga Takara

2. Zanga-zanga a wasu jihohin Nijeriya: Zanga-zangar ta bazu zuwa jihohi da dama, inda ’yan Nijeriya suka buƙaci gyara a rundunar ’yansanda da ingantaccen shugabanci.

3. Tallafa wa jama’a: Fitattun mutane da sauran ’yan Nijeriya sun tallafa wa masu zanga-zangar da abinci, ruwa, kayan agajin gaggawa da sufuri.

4. Jan hankalin duniya: Taken #EndSARS ya shahara a duniya, inda fitattun mutane da kafafen yaɗa labarai na ƙasashen waje suka nuna goyon bayansu ga masu zanga-zangar.

5. Hoton Aisha Yesufu: Wani hoto da ya bazu na fitacciyar ’yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu, ta ɗaga hannunta sama ya zama alamar jarumta da yin tsayin daka wajen neman adalci.

6. Sanya dokar hana fita: Gwamnatocin wasu jihohi sun sanya dokar hana fita yayin da rikici da tashin hankali suka ɓarke.

7. Kisan jami’an ’yansanda: An kai wa wasu jami’an ’yansanda hari tare da kashe a lokacin rikicin.

8. Lalata kadarorin gwamnati da na jama’a: An kai hare-hare kan gine-ginen gwamnati, ofisoshin ’yansanda, gidajen yaɗa labarai da wuraren kasuwanci, yayin da aka fasa wasu shaguna.

Shekaru shida bayan faruwar lamarin, zanga-zangar #EndSARS na ci gaba da kasancewa muhimmin tarihi a Nijeriya, tare da tunatar da jama’a buƙatar yin adalci, gaskiya, ɗora wa masu laifi alhaki da kawo ƙarshen cin zarafin jama’a da jami’an ’yansanda.

MASU ALAKA

Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya
Rahotonni

Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya

October 13, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC
Rahotonni

Jam’iyyu Da Ƴan Takara Sun Yi Wa INEC Bore Kan Cire Sunayensu Daga Takara

October 12, 2026
Hanyoyi 5 Da Za A Sayi Fetur Mai Rahusa A Gidajen Man NNPC
Manyan Labarai

Hanyoyi 5 Da Za A Sayi Fetur Mai Rahusa A Gidajen Man NNPC

October 10, 2026
Next Post
CMG Da Gwamnatin Lardin Jiangsu Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar  “Shirin Karfafa Manyan Kamfanoni”

CMG Da Gwamnatin Lardin Jiangsu Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar “Shirin Karfafa Manyan Kamfanoni”

LABARAI MASU NASABA

ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Sun Haifar Da Yunwa Da Talauci A Nijeriya, Muna Ƙoƙarin Kawar Da Su – Tinubu

Sun Haifar Da Yunwa Da Talauci A Nijeriya, Muna Ƙoƙarin Kawar Da Su – Tinubu

October 24, 2026
Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

October 24, 2026
Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci

Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci

October 24, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC

Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC

October 24, 2026
Hukumar Zaɓe Ta Wayar Da Kan Nakasassu Kan Kaɗa Ƙuri’a A Zamfara

Hukumar Zaɓe Ta Wayar Da Kan Nakasassu Kan Kaɗa Ƙuri’a A Zamfara

October 24, 2026
Tinubu Ya Ce Ba Zai Iya Raka ‘Yan Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa Kowace Jiha Ba

Me Tinubu Zai Yi Wa Arewa Alƙawari A Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓensa A Kaduna?

October 24, 2026
Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.