Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kaftin din tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagle Ahmed Musa, na shirin kulla yarjejeniya da kungiyar West Brom dake buga gasar Premier ta Ingila.
Rahotanni sun ce ana sa ran yau Laraba Ahmad Musa zai yi tattaki zuwa Ingila domin tantance lafiyar sa kafin rattaba hannu kan yarjejeniyar da majiyoyi suka ruwaito cewar ba mai tsawo bace.
A halin yanzu kungiyar West Bromwich Albion ce ta 19 a gasar Premier da maki 11 sakamakon rashin kokarin kungiyar wanda ta kai sai da ta kori mai koyarwar ta a cikin watan Disamba kuma ta maye gurbinsa da Sam Allarddyce.
A shekarar 2016 Ahmed Musa ya rabu da kungiyar kwallon kafa ta CSKA Moscow dake kasar Rasha, bayan ci mata kwallaye 55 a wasanni 167 da ya buga mata, inda ya koma kungiyar Leicester City a shekarar.
Bayan rashin samun lokacin buga wasa a kungiyar Leicester City, Ahmad ya sake komawa CSKA Moscow a matsayin aro, daga nan kuma ya koma kungiyar Al Nassrr dake Saudiya a watan Janairun shekara ta 2019, inda a watan Oktoban bara ya rabu da kungiyar, kawo yanzu kuma ba ya tare da wata kungiya, sai wadda yake shirin kullawa da West Brom.