A karon farko, Kungiyar ci gaban Zabarmawa (ZADA) ta gudanar da babban taronta na kasa da kuma kaddamar da asusun zunzurutun kudi har naira miliyan 100, a filin wasa da ke Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.
Taron wadda ya tattaro dukkan al’ummar Zabarmawa da ke jihohi 36 a Nijeriya da babban birnin tarayya, (Abuja) da kuma sauran kasashen da ke makwabtaka da Nijeriya.
- Ranar Malaman Kasar Sin: Menene Sirrin Ci Gaban Kasar Sin?
- Takaddama Kan Shirin Daukar Sabbin ‘Yansanda
Da yake jawabi a wajen taron, Sarkin Zabarmawan Jihar Legas, Alhaji Aliyu Abubakar, ya bayyana farin cikinsa duba da yadda al’ummar Zabarmawa daga sassa daban-daban na Nijeriya da kasashe makwabta suka amsa kira.
Ya ce wannan alama ce da ke nuna cewa al’ummar Zabarmawa ‘yan asalin kasar nan ne, saBanin yadda wasu ke kallonsu a matsayin baki daga wasu kasashe, musamman jamhuriyar Nijar.
Alhaji Abubakar ya kuma kara da cewa Zabarmawa suna ba da gagarumin gudunmawa wajen bunkasar tattalin arziki, siyasa da kuma zamantakewar kasar nan.
Ya yi kira ga ilahirin al’ummar Zabarmawan da su hada kawunansu a duk inda suke a Nijeriya da sauran kasashe, domin ganin sun zama tsintsiya madaurinki daya, sannan ya jinjina wa kungiyar ci gaban al’ummar Zabarmawan (ZADA) a bisa shirya kasaitaccen taro karo na farko a garin Birnin Kebbi.