Assalamu alaikum, malam ko ya halatta na yi wa Mahaifina Layya bayan ya mutu don kawai na kyautata masa?
Wa’alaikumus salam, Ya halatta ka yi masa, saboda sadaka ce, sadaka kuma ta halatta ga mamaci, zai kuma iya samun ladanta, saboda hadisai sun tabbatar da cewa mamaci yana iya amfana da sadakar rayayye ya masa.
Amma ba a son dawwama a kan hakan, saboda bai inganta Annabi (SAW) ya yi wa wani matacce shi kadai Layya ba, ya kasance yana mutukar son Hamza baffansa, amma bayan an kashe shi, bai taba yi masa Layya ba, sai dai yakan yi Layya ga Ahalin gidansa da wanda bai yi layya ba daga cikin Al’umarsa.
Don neman karin bayani duba Bada’i’ussana’iu 5/72 da kuma madalibu ulinnuhaa 2/472
Allah ne mafi sani.