ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zargin Maita: ‘Yansanda Sun Cafke Mutum Huɗu Bisa Hallaka Wani A Bauchi

by Khalid Idris Doya
7 hours ago
Maita

Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta kama wasu mutane huɗu da ake zargi da kashe wani mutum mai shekaru 45 a duniya, Garba Abdullahi, bayan an zargesa da maita a ƙauyen Dunari da ke gundumar Atahowa, ƙaramar hukumar Itas/Gadau ta jihar.

A cewar ‘yansandan, a ranar 22 ga Satumba, 2026, wani mazaunin ƙauyen Dunari mai shekaru 35 ya kai rahoto ofishin ‘yansanda na Gadau, inda ya bayyana cewa an kai wa ɗan uwansa, Garba Abdullahi, hari a kan hanyarsa ta dawowa gida daga gona.

Mai kai ƙorafin ya ce mutane huɗu ne suka kai wa ɗan uwan nasa harin, inda suka zarge shi da maita a kan wata mata mai suna Sawaida Dahiru da ya janyo mata rashin lafiya.

ADVERTISEMENT

‘Yansanda sun bayyana waɗanda ake zargin da Shitu Dahiru, mai shekaru 25; Magaji Dahiru, mai shekaru 42; Sabi’u Auwalu, mai shekaru 20; da Abbah Abdulzahar, mai shekaru 19.

An zargi mutum huɗun da cewa sun daɓa wa Abdullahi wuƙa tare da sara masa adda a sassa daban-daban na jikinsa, lamarin da ya sa ya suma.

LABARAI MASU NASABA

Sultan Ya Gargaɗi Malaman Addini Kan Kare Masu Cin Hanci Da Rashawa

’Yansanda Sun Ƙwato Motoci 52, Sun Kama Masu Laifi 177 A Mako Guda

A cikin sanarwa da Kakakin Rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi, SP Nafiu Habib, ya fitar a ranar Laraba, ya ce bayan samun rahoton, jami’an ’yansanda sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka ɗauki wanda aka jikkata zuwa babban asibitin Azare domin samun kulawar gaggawa.

Ya ce daga bisani, likita ya tabbatar da mutuwar Abdullahi, sannan aka miƙa gawarsa ga ’yan uwansa domin yi masa jana’iza.

Maita
Khalid Idris Doya
+ postsBio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Basukan Giratuti: Gwamnatin Bauchi Ta Fara Biyan ₦10bn Ga ‘Yan Fansho 1,700
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Zaɓen Cike Gurbi: Gwamnatin Bauchi Ta Yi Allah-wadai Da Kama Masu Kaɗa Ƙuri’a
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi

MASU ALAKA

Sultan
Manyan Labarai

Sultan Ya Gargaɗi Malaman Addini Kan Kare Masu Cin Hanci Da Rashawa

September 23, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi
Labarai

’Yansanda Sun Ƙwato Motoci 52, Sun Kama Masu Laifi 177 A Mako Guda

September 23, 2026
Sultan
Labarai

Kada Ku Ɗauki Nauyin Aikin Hajji Da Kuɗaɗen Da Aka Sace — Sultan Ga ’Yan Siyasa

September 23, 2026
Next Post
Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

LABARAI MASU NASABA

Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

September 23, 2026
Zargin Maita: ‘Yansanda Sun Cafke Mutum Huɗu Bisa Hallaka Wani A Bauchi

Zargin Maita: ‘Yansanda Sun Cafke Mutum Huɗu Bisa Hallaka Wani A Bauchi

September 23, 2026
Dandalin Al’adu Na Beijing Zai Mayar Da Hankali Ga Batun Gadon Al’adu Da Koyi Da Juna Tsakanin Mabanbantan Wayewar Kai

Dandalin Al’adu Na Beijing Zai Mayar Da Hankali Ga Batun Gadon Al’adu Da Koyi Da Juna Tsakanin Mabanbantan Wayewar Kai

September 23, 2026
Sultan

Sultan Ya Gargaɗi Malaman Addini Kan Kare Masu Cin Hanci Da Rashawa

September 23, 2026
Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Taron Nuna Kwarewar Sana’o’i Na Duniya Na Shekarar 2026

Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Taron Nuna Kwarewar Sana’o’i Na Duniya Na Shekarar 2026

September 23, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Ƙwato Motoci 52, Sun Kama Masu Laifi 177 A Mako Guda

September 23, 2026
Yayin Da Taron UNGA Na 81 Ya Zo A Lokacin Da Duniya Ta Shiga Tsaka-mai-wuya…

Yayin Da Taron UNGA Na 81 Ya Zo A Lokacin Da Duniya Ta Shiga Tsaka-mai-wuya…

September 23, 2026
Sultan

Kada Ku Ɗauki Nauyin Aikin Hajji Da Kuɗaɗen Da Aka Sace — Sultan Ga ’Yan Siyasa

September 23, 2026
Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana

Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana

September 23, 2026
Basukan Giratuti: Gwamnatin Bauchi Ta Fara Biyan ₦10bn Ga ‘Yan Fansho 1,700

Basukan Giratuti: Gwamnatin Bauchi Ta Fara Biyan ₦10bn Ga ‘Yan Fansho 1,700

September 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.