ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi

by Sulaiman and Khalid Idris Doya
2 months ago
Bauchi

Rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar wani yaro mai shekaru 13 a duniya, Mubarak Mohd, sakamakon ɗanna kunamar wata bindiga ƙirar gida (Dane) wa kansa da kansa a ƙauyen Udubo, karamar hukumar Gamawa ta jihar.

A cewar rundunar, lamarin ya faru ne a ranar 5 ga Satumba, 2026, lokacin da wani mafarauci mai shekaru 35, Suleiman Hamza, wanda ke zaune a ƙauyen, ya dawo daga farauta, inda ake zargin ya yi sakacin barin bindigar shaƙe da harsashi a cikin ɗakinsa tare da yin fitarsa.

Bauchi

’Yansandan sun ce daga bisani Mubarak ya shiga ɗakin, inda ake zargin ya ja kunamar bindigar, lamarin da ya sa ta tashi ta kuma ji masa mummunan rauni da ya yi sanadin mutuwarsa.

ADVERTISEMENT

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar ranar Lahadi, ya ce bayan samun rahoton lamarin, jami’an bincike na sashen ’yansanda na Gamawa sun gaggauta zuwa wurin da abin ya faru tare da fara gudanar da binciken farko.

Ya ce an garzaya da yaron zuwa babban asibitin Gamawa, inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwarsa.Sanarwar ta ce, “An ɗauki hotunan gawar, sannan aka miƙa ta ga ’yanuwansa domin mata jana’iza da biso bisa tsarin addinin Musulunci.”

LABARAI MASU NASABA

Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci

Rundunar ta ƙara da cewa an kama wanda ake zargi, daga bisani an miƙa kes ɗin zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar (SCID) domin gudanar da cikakken bincike.

A wani labarin kuma, rundunar ta ce jami’anta sun daƙile wani yunƙurin fashi da makami a kan hanyar Kajala-Kere, da ke wajen garin Burra, tare da kwato babura biyu da ake zargin ‘yan fashin sun sace.

SP Habib ya ce a ranar 5 ga Satumba, ’yansanda sun samu rahoto daga jami’in da ke kula da ofishin ’yansanda na Kajala cewa wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, ɗauke da adduna da sanduna, sun tare hanyar Kajala-Kere.

Ya ce waɗanda ake zargin sun kwace babura ƙirar Bajaj guda biyu, wayoyin Android guda biyu da kuma power bank daga hannun Ado da wasu mazauna ƙauyen Kere guda uku.Bayan samun rahoton, an hado kan jami’an ’yansanda daga sashen Burra da jami’an sa-kai na yankin, inda aka gaggauta tura su wurin da lamarin ya faru.

A cewarsa, waɗanda ake zargin sun tsere ne bayan ganin jami’an tsaro, inda suka bar baburan da suka sace, tare da daƙile yunƙurin ci gaba da fashin.Jami’an sun kwato baburan, sannan suka binciki dazuzzukan da ke kewaye da wurin domin ƙoƙarin cafke waɗanda suka tsere.

Kwamishinan ‘yansandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yaba wa jami’an da suka mayar da tunƙari ‘yan fashin cikin gaggawa, wanda ya ce hakan ya taimaka wajen daƙile fashin.

Sai dai kwamishinan ya bayyana damuwarsa kan mutuwar yaron da ya harbi kansa a Gamawa, inda ya gargaɗi mafarauta da sauran masu mallakar bindigogi da su riƙa kula da makamai sosai tare da tabbatar da cewa an ajiye bindigogi a wuraren da yara ba za su iya isa gare su ba.

Kwamishinan ya kuma buƙaci mazauna jihar da su ci gaba da bai wa ’yansanda sahihan bayanai cikin lokaci, yana mai tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da kokarin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.

Bauchi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Ya Rantsar Da Manyan Sakatarori Biyar
  • Sulaiman
    Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Djibouti
  • Sulaiman
    Ta Yaya Ake Ci Gaba Da Fitar Da Sabbin Kayayyaki A Yayin Baje Koli Na Canton Fair
Bauchi
Khalid Idris Doya
+ posts Bio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    2027: Mazauna Bauchi Sun Ƙalubalanci Iƙirarin Limami Na Cewa An Cire Shi Saboda Tallar Tinubu
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Rikicin Cikin Gida Ya Ɓarke A Jam’iyyar APM, Wani Ɓangare Ya Tsige Shugaban Jam’iyyar A Bauchi

MASU ALAKA

Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
Labarai

Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

October 24, 2026
Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci
Manyan Labarai

Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci

October 24, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC
Labarai

Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC

October 24, 2026
Next Post
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

Hukumar Zaɓe Ta Wayar Da Kan Nakasassu Kan Kaɗa Ƙuri’a A Zamfara

Hukumar Zaɓe Ta Wayar Da Kan Nakasassu Kan Kaɗa Ƙuri’a A Zamfara

October 24, 2026
Tinubu Ya Ce Ba Zai Iya Raka ‘Yan Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa Kowace Jiha Ba

Me Tinubu Zai Yi Wa Arewa Alƙawari A Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓensa A Kaduna?

October 24, 2026
Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

October 24, 2026
Magoya Bayan ‘Tinubu Must Come’ Da ‘Tinubu Must Go’ Sun Yi Arangama

Magoya Bayan ‘Tinubu Must Come’ Da ‘Tinubu Must Go’ Sun Yi Arangama

October 24, 2026
MDPCO Ta Soki Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Kaduna

MDPCO Ta Soki Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Kaduna

October 24, 2026
Zaɓen 2027 Ba Kamar Na 2023 Ba Ne, Wannan Karon Ƙuri’un Kaduna Na Tinubu Ne — Gwamna Uba Sani

Zaɓen 2027 Ba Kamar Na 2023 Ba Ne, Wannan Karon Ƙuri’un Kaduna Na Tinubu Ne — Gwamna Uba Sani

October 24, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 245, Ta Raba 214,997 Da Muhallansu A 2026 – NEMA

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 245, Ta Raba 214,997 Da Muhallansu A 2026 – NEMA

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.