Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Bauchi ta yi watsi da rahotannin da ke cewa tsarin jam’iyyar a jihar ya rushe ya koma cikin jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), inda ta bayyana iƙirarin a matsayin ƙarya da kuma aikin wasu masu sojar-gona.
Mai ba jam’iyyar shawara kan harƙoƙin shari’a, Barista Yahaya Garkuwa, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani taron manema labarai da ya gudana a sakatariyar PDP da ke samun goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike, da ke kan titin Maiduguri Bypass, Bauchi.
Garkuwa ya ce jam’iyyar PDP da doka ta amince da ita a Jihar Bauchi ita ce wadda Hon. Ibrahim Kassim Toro ke jagoranta, yayin da a matakin ƙasa jam’iyyar ke ƙarƙashin jagorancin Hon. Abdulrahman Mohammed.
Ya bayyana cewa an daɗe ana kai rikicin shugabancin jam’iyyar gaban kotuna, inda kotuna daban-daban suka tabbatar da tsarin shugabancin da jam’iyyar ta amince da Abdulrahman.
A cewarsa, babbar kotun tarayya ta taɓa tabbatar da kwamitin riƙon kwarya da Abdulrahman Mohammed ke jagoranta a matsayin sahihin shugabancin PDP a matakin ƙasa.
Ya ce daga bisani ɓangaren Tanimu Turaki ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin, amma kotun ɗaukaka ƙarar ta tabbatar da hukuncin, tare da amincewa da shugabancin Abdulrahman Mohammed a matakin ƙasa da kuma shugabancin Ibrahim Kassim Toro a Jihar Bauchi.
Garkuwa ya ƙara da cewa daga ƙarshe an kai batun gaban Kotun Ƙoli bayan ɓangaren adawa ya nuna rashin gamsuwa da hukuncin kotun daukaka kara.
Ya yi iƙirarin cewa hukuncin Kotun Ƙoli ya ƙara tabbatar da matsayinsu, inda ya ce ɓangaren Tanimu Turaki ba shi da goyon bayan doka.
Mai ba jam’iyyar shawara kan harkokin shari’ar ya zargi ɓangaren da ke adawa da su da komawa yin sojan-gonar shugabannin jam’iyyar da kuma yaɗa labaran ƙarya game da PDP bayan sun kare dukkan hanyoyin shari’ar da suke da su.
Ya ce, “Yanzu da hukuncin Kotun Ƙoli ya rufe musu duk wata hanya, sun fara sojan-gonar cewa su ne shugabannin PDP. Sun yanke shawarar haifar da ruɗani ta hanyar gaya wa jama’a cewa tsarin PDP ya rushe ya koma APM.”
Garkuwa ya jaddada cewa sahihan mambobin PDP suna nan cikin jam’iyyar kuma ba su fice zuwa wata jam’iyyar siyasa ba. “Mu, sahihan mambobin PDP, muna nan cikin PDP. Ba mu shiga wata jam’iyyar siyasa ba; har yanzu muna cikin PDP.”
Ya kuma bayyana cewa shugabancin PDP na Bauchi na shirin ɗaukar matakin shari’a kan wasu mutane da ake zargin suna bayyana kansu a matsayin jami’an jam’iyyar ba tare da izini ba.
Garkuwa ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da jita-jitar cewa PDP ta haɗe da wata jam’iyya, yana mai jaddada cewa PDP ita ce jam’iyyar da doka ta amince da ita a jihar.
Ya kuma ƙalubalanci ɓangaren da ke adawa da su da ya bayyana sunayen ‘yan takarar da ya ce sun tsayar domin shiga zaɓen shekarar 2027.
Ya ce, “Idan da gaske su mambobin PDP ne, su bayyana sunayen ‘yan takararsu. Ba su da ‘yan takara.”
Garkuwa ya tabbatar wa magoya bayan jam’iyyar cewa PDP tana nan daram kuma a shirye take ta shiga babban zaben shekarar 2027. “PDP ba ta rushe zuwa wata jam’iyyar siyasa ba. PDP tana nan daram, PDP tana da ƙarfi kuma tana cikin shiri tsaf domin babban zaben shekarar 2027.”
Mai ba jam’iyyar shawara kan harkokin shari’ar ya samu rakiyar shugaban jam’iyyar na jiha, da sauran jami’an jam’iyyar, masu ruwa da tsaki da kuma magoya baya a wajen taron manema labaran.
Ya jaddada cewa PDP ta tsayar da ‘yan takara masu nagarta waɗanda za su iya samun nasara a zaben, inda ya tuna cewa jam’iyyar ce ta aiwatar da wasu daga cikin muhimman ayyukan ci gaba a Jihar Bauchi da kuma faɗin ƙasar nan a lokacin da take mulki.
Ya bayyana cewa Peoples Democratic Party (PDP) ta tsayar da Hon. Usman Adamu Ahmed Suphi a matsayin ɗan takararta na gwamna a Jihar Bauchi a babban zaben shekarar 2027, yayin da Alhaji Abdulkadir Aliyu Bababa zai kasance mataimakinsa.













