• Leadership Hausa
Friday, August 12, 2022
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Daga Birnin Sin

Shiru-Shiru Ba Tsoro Ba Ne…

by CMG Hausa
2 months ago
in Daga Birnin Sin
0
Shiru-Shiru Ba Tsoro Ba Ne…
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A duk lokacin da aka kira taruka kama daga na tattalin arziki, al’adu, ko wasanni ko Ilimi ko kare muhalli ko harkar tsaro, walau a mataki na kasa ko shiyya ko kasa da kasa, muhimman abubuwan da mahalarta tarukan ke tattaunawa, su ne matsaloli da nasarori da aka cimma a wadannan fannoni, gami da sabbin dabaru ko matakai da aka bijiro da su don inganta su, wadda daga karshe za su taimaka wajen haifar da kyakkyawan sakamako da ma burin da ake fatan cimmawa, wanda zai amfani duniya baki daya.

Sai dai wani abin mamaki shi ne, yayin taron tsaro na Shangri-La karo na 19 da ya gudana a kasar Singapore, maimakon a mayar da hankali kan yadda za a inganta matakan tsaro da zai amfani duniya baki daya, sai Amurka da wasu kawayenta suka mayar da hankali kawai wajen neman shafawa kasar Sin baken fenti da ma tsoma baki a harkokin cikin gidanta. Wannan ya sa ministan tsaron kasar Sin Wei Fenghe, yayin da yake gabatar da nasa jawabin a wajen taron, ya nunawa masu irin wannan mugun nufi kan kasar Sin cewa, shiru-shiru fa ba tsoro ba ne…

Sakon da minista Wei ya gabatar, ya kara tunatar da bangaren Amurka da ma duniya baki daya cewa, yanzu huldar da ke tsakanin kasashen 2 tana cikin wani muhimmin lokaci, kuma kyakkyawar huldar da ke tsakaninta da Amurka ta dace da muradunsu da ma duniya baki daya.

Amma idan har Amurka ta nace da neman tayar da rikici tsakaninta da Sin, to hakan ba zai kawo musu da ma kasashen duniya alheri ba. Haka kuma bai dace ba Amurka da kawayenta su rika ayyana kasar Sin a matsayin wai mai takara da Amurka ko barazana, idan kuma suka yi hakan, hakika za ta yi mummunan kuskure. Idan kunne ya ji, to gangan jiki ya tsira.

Kasar Sin dai ta bukaci Amurka da ta daina shafa mata kashin kaji, da neman dakile ci gaban ta, kana ta daina tsoma baki a harkokin cikin gidanta, da kuma illanta muradun kasar Sin.

Labarai Masu Nasaba

Kungiyar Kawance Ta Sin Da Niger Na Goyon Bayan Manufar Sin Daya Tak

Wang Wenbin: Duk Irin Sauyin Yanayi Sin Za Ta Wanzar Da Fadada Bude Kofa

Wani muhimmin batu da Amurka da sauran masu neman ballewar yankin Taiwan ya dace su fahimta da kunnen basira shi ne, sake hadewar Taiwan da babban yanki cikin lumana, shi ne babban fatan al’ummar Sinawa. Kuma duk wanda ya kuskura ya nemi tayar da batun ballewar yankin Taiwan daga kasar Sin, kasar Sin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen mayar da duk wani martani ko ta halin kaka. Domin yaro bai san wuta ba, sai ya taka.

Masu fashin baki na kara jaddada cewa, wajibi ne Sin da Amurka su tattauna da juna, su mutunta juna, su kuma zauna tare cikin lumana, su hada kansu domin samun moriyar juna, amma idan Amurka ta nemi yin fito-na-fito da Sin, to, kasar Sin ta sha nanata cewa, ba za ta yarda a yi mata sakiyar da babu ruwa ba. (Ibrahim)

ShareTweetSendShare
Previous Post

Zargin Yada Luwadi: Saudiyya Ta Hana Sayar Da Kayan Wasa Na Yara Masu Siffanta Jinsin Mutum

Next Post

NDLEA Ta Kwace Kwaya Mai Nauyin Kilo 4,520 A Jihar Zamfara

Related

Kungiyar Kawance Ta Sin Da Niger Na Goyon Bayan Manufar Sin Daya Tak
Daga Birnin Sin

Kungiyar Kawance Ta Sin Da Niger Na Goyon Bayan Manufar Sin Daya Tak

6 mins ago
Wang Wenbin: Duk Irin Sauyin Yanayi Sin Za Ta Wanzar Da Fadada Bude Kofa
Daga Birnin Sin

Wang Wenbin: Duk Irin Sauyin Yanayi Sin Za Ta Wanzar Da Fadada Bude Kofa

51 mins ago
Shugaba Xi Ya Yi Kira Ga Sassan Kasa Da Kasa Da Su Yi Hadin Gwiwar Samar Da Ci Gaban Duniya
Daga Birnin Sin

Shugaba Xi Ya Yi Kira Ga Sassan Kasa Da Kasa Da Su Yi Hadin Gwiwar Samar Da Ci Gaban Duniya

2 hours ago
Hanyoyin Jiragen Kasa Da Sin Ta Gina Sun Zama Shaidar Raya Shirin “Ziri Daya Da Hanya Daya”
Daga Birnin Sin

Hanyoyin Jiragen Kasa Da Sin Ta Gina Sun Zama Shaidar Raya Shirin “Ziri Daya Da Hanya Daya”

3 hours ago
Yunkurin Amurka Kan Sana’ar Kera Sassan Na’urorin Laturoni Ba Zai Yi Nasara Ba
Daga Birnin Sin

Yunkurin Amurka Kan Sana’ar Kera Sassan Na’urorin Laturoni Ba Zai Yi Nasara Ba

4 hours ago
Akwai Alamun Ba Gudu Ba Ja Da Baya A Kan Batun Taiwan
Daga Birnin Sin

Akwai Alamun Ba Gudu Ba Ja Da Baya A Kan Batun Taiwan

6 hours ago
Next Post
NDLEA Ta Kwace Kwaya Mai Nauyin Kilo 4,520 A Jihar Zamfara

NDLEA Ta Kwace Kwaya Mai Nauyin Kilo 4,520 A Jihar Zamfara

LABARAI MASU NASABA

Kungiyar Kawance Ta Sin Da Niger Na Goyon Bayan Manufar Sin Daya Tak

Kungiyar Kawance Ta Sin Da Niger Na Goyon Bayan Manufar Sin Daya Tak

August 12, 2022
Da Dumi-Dumi: ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sace Buhari Da El-Rufai 

Rashin Tsaro Na Kawo Koma Baya Ga Tattalin Arzikin Nijeriya – Buhari

August 12, 2022
Wang Wenbin: Duk Irin Sauyin Yanayi Sin Za Ta Wanzar Da Fadada Bude Kofa

Wang Wenbin: Duk Irin Sauyin Yanayi Sin Za Ta Wanzar Da Fadada Bude Kofa

August 12, 2022
Shugaba Xi Ya Yi Kira Ga Sassan Kasa Da Kasa Da Su Yi Hadin Gwiwar Samar Da Ci Gaban Duniya

Shugaba Xi Ya Yi Kira Ga Sassan Kasa Da Kasa Da Su Yi Hadin Gwiwar Samar Da Ci Gaban Duniya

August 12, 2022
Zan Biya Wa ASUU Bukatunsu Idan Na Zama Shuagaban Kasa – Atiku

Zan Biya Wa ASUU Bukatunsu Idan Na Zama Shuagaban Kasa – Atiku

August 12, 2022
Hanyoyin Jiragen Kasa Da Sin Ta Gina Sun Zama Shaidar Raya Shirin “Ziri Daya Da Hanya Daya”

Hanyoyin Jiragen Kasa Da Sin Ta Gina Sun Zama Shaidar Raya Shirin “Ziri Daya Da Hanya Daya”

August 12, 2022
Yunkurin Amurka Kan Sana’ar Kera Sassan Na’urorin Laturoni Ba Zai Yi Nasara Ba

Yunkurin Amurka Kan Sana’ar Kera Sassan Na’urorin Laturoni Ba Zai Yi Nasara Ba

August 12, 2022
Hisbah Ta Jadadda Muhimmancin Gwajin Lafiya Kafin Aure 

Hisbah Ta Jadadda Muhimmancin Gwajin Lafiya Kafin Aure 

August 12, 2022
Shugaba Buhari Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro A Nijeriya -Buratai

Shugaba Buhari Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro A Nijeriya -Buratai

August 12, 2022
Gwamnatin Tarayya Ta Ware Biliyan 2.6 Domin Tsaron Abuja

Daga Asabar 8 Zuwa Talata 11 Ga Watan Muharram 1444

August 12, 2022
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.