ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NNGF Ta Kaddamar Da Kwamitin Amintattu Na Gidauniyar Asusun Tsaro Ta Yankin

by Sulaiman
2 months ago
Arewa

Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewacin Nijeriya (NNGF) da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa sun sake jaddada aniyarsu ta magance matsalar rashin tsaro a yankin, inda suka bayyana goyon bayansu ga kafa rundunar ’yansandan jihohi tare da amincewa da wasu sabbin matakai domin magance tushen matsalolin tashin hankalin.

An bayyana hakan ne a cikin sanarwar bayan taron haɗin gwiwa da aka gudanar ranar Laraba a Gidan Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna, inda gwamnoni da sarakunan gargajiya suka yi nazari kan halin tsaron Arewacin Nijeriya.

Taron ya yaba wa Bola Ahmed Tinubu bisa ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen magance matsalolin tsaron ƙasa, tare da yin alƙawarin ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro na tarayya ta hanyar inganta musayar bayanan sirri, ƙarfafa juriyar al’umma da kuma haɓaka haɗin gwiwar jihohin Arewa.

ADVERTISEMENT

Taron ya bayyana cewa idan aka horar da ’yansandan jihohi yadda ya kamata, aka tanade su da kayan aiki tare da ba su cikakken goyon baya, hakan zai taimaka matuƙa wajen yaƙi da rashin tsaro a faɗin ƙasar.

Taron ya kuma bayyana amincewarsa da sabon Kwamitin Amintattu na Gidauniyar Asusun tsaro ta Arewacin Nijeriya, tare da buƙatar mambobinsa su gudanar da aikinsu cikin adalci, gaskiya da ’yancin kai.

LABARAI MASU NASABA

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

Gwamnonin sun yabawa jihohin da suka cika alƙawarinsu na bayar da gudummawar Naira biliyan ɗaya a kowane wata ga Asusun Tallafin Tsaro, suna mai cewa hakan alama ce ta haɗin kai da ɗaukar nauyin kare yankin baki ɗaya. Sun kuma yi kira ga sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin fararen hula, kafafen yaɗa labarai da sauran al’umma su mara wa asusun baya.

Baya ga matakan tsaro, taron ya amince da ɗaukar matakan magance tushen matsalolin rashin tsaro, ciki har da talauci, rashin aikin yi, jahilci da yawaitar yara marasa zuwa makaranta. A saboda haka, ya yi alƙawarin ƙara zuba jari a fannonin ilimi, noma, ƙarfafa matasa, koyar da sana’o’i da samar da hanyoyin samun abin yi domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Dangane da daminar bana, taron ya buƙaci gwamnatoci da hukumomin tsaro su tabbatar da tsaron manoma yayin aikin gona, tare da yin aiki tare da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma domin hana rikice-rikicen da ka iya tasowa. Haka kuma, ya bayyana goyon bayansa ga bunƙasa kiwo da zamanantar da harkokin noma domin inganta rayuwar al’umma da bunƙasa tattalin arzikin yankin.

A ƙarshe, taron ya amince da faɗaɗa haɗin gwiwar jihohin Arewa zuwa sauran muhimman fannoni kamar ilimi, noma da lafiya, ta hanyar samar da tsari guda domin inganta ayyukan gwamnati da hanzarta ci gaban yankin.

Arewa
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • Sulaiman
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
  • Sulaiman
    Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

MASU ALAKA

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
Labarai

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO
Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana
Labarai

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Next Post
Badaƙalar PFIPC: Ban Taɓa Haɗuwa Da Gbajabiamila Ba – Adeyemi

Badaƙalar PFIPC: Ban Taɓa Haɗuwa Da Gbajabiamila Ba - Adeyemi

LABARAI MASU NASABA

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.