ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Badaƙalar PFIPC: Ban Taɓa Haɗuwa Da Gbajabiamila Ba – Adeyemi

by Sadiq
2 months ago

Tsohon Darakta Janar na Hukumar Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), Prince Mathew Adeniyi Adeyemi, ya musanta cewa ya taɓa ganawa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ido da ido.

Adeyemi ya ce bincike mai zaman kansa ne kawai zai iya gano gaskiyar zargin da ke tattare da hukumar.

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta fitaccen mai amfani da Kafafen Sada Zumunta, Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan, inda ya ce ba zai iya tabbatarwa ko Gbajabiamila na da hannu a lamarin ba.

ADVERTISEMENT

Ya ce bai taɓa yin ganawar sirri da Gbajabiamila ba, amma ya yi iƙirarin cewa ya yi magana da wani mutum da yake ganin shi ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasar sau uku ta waya ta hannun, Dolapo Tanimola.

Sai dai Adeyemi ya amince cewa ba zai iya tabbatar da cewa mutumin da ya yi magana da shi, shi ne Gbajabiamila ba, saboda ba su yi magana ta bidiyo ba.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Lokacin da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar Gbajabiamila ba shi da hannu a lamarin, Adeyemi ya amince da hakan, yana mai cewa ba shi da ikon cewa Shugaban Ma’aikatan ya yi ƙarya ko kuma ya faɗi gaskiya.

Ya ce wannan rashin tabbaci ne ya sa yake kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya kafa bincike mai zaman kansa domin gano gaskiya.

A yanzu haka Adeyemi na fuskantar shari’a a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zarge-zargen da suka shafi gudanar da PFIPC, wadda Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa babu ita.

Ana sa ran ci gaba da sauraron shari’ar a ranar 14 ga watan Yuli.

Taƙaddama ta ƙara ƙamari ne bayan Adeyemi ya zargi Gbajabiamila da neman kashi 48 cikin 100 na tallafin aiki na hukumar wanda ya kai Naira biliyan 27.4, da kuma karɓar Naira miliyan 400 da ya danganta da wasu naɗe-naɗe a hukumar.

Sai dai Gbajabiamila ya musanta zargin, yana cewa bai taɓa yin wata hulɗa da Adeyemi kai tsaye ko ta hannun wani ba, kuma ya yi barazanar ɗaukar matakin shari’a kan zargin.

A halin yanzu, Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da gabatar masa da rahoto cikin kwanaki 30.

Haka kuma Adeyemi ya bayyana cewa yana shirin miƙa kansa ga Rundunar ’Yansandan Nijeriya ko kuma Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS).

MASU ALAKA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
Manyan Labarai

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Next Post
Damar Fita Daga Kangin Dalar Amurka Ta Sake Samuwa Ga Kasashen Afirka

Damar Fita Daga Kangin Dalar Amurka Ta Sake Samuwa Ga Kasashen Afirka

LABARAI MASU NASABA

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.