ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƙungiyar Kwankwasiyya Ta Soki Shirin Karɓo Bashin Biliyan 55 A Kano

by Abubakar Sulaiman
4 days ago

Ƙungiyar Kwankwasiyya ta nuna matuƙar damuwa tare da yin watsi da shirin Gwamnatin Jihar Kano na tilasta wa ƙananan hukumomin jihar 44 karɓar rancen kuɗi da ya kai kimanin Naira biliyan 55 daga wani banki.

Kakakin ƙungiyar, Dokta Habibu Saleh Mohammed, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Kano a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, 2026, inda ya buƙaci a tabbatar da gaskiya, da riƙon amana, da bin doka kafin ɗaukar wannan mataki.

A cewar ƙungiyar, bayanan da ke ƙasa sun nuna cewa ana son kowace ƙaramar hukuma ta karɓi bashin kusan Naira biliyan 1.3, wanda aka tsara kashe Naira miliyan 632.57 wajen gina cibiyoyin jarrabawar kwamfuta (CBT), Naira miliyan 117.41 don shirin tallafawa al’umma, da kuma Naira miliyan 500 don wani aiki da ba a bayyana sunansa ba.

ADVERTISEMENT

Kwankwasiyya ta buƙaci cikakken bayani kan inda za a kafa waɗannan cibiyoyi, da sunan wanda ya yi ƙididdigar kuɗaɗen, da kuma bayanin ainihin aikin da aka keɓe wa Naira miliyan 500 ba tare da sanar da al’umma ba.

Dokta Mohammed ya kuma soki lokacin da aka zaɓa domin ciyo wannan rance, yana mai nuni da cewa gabatowar kakar zaɓe ya sa batun ke haifar da shakku kan yiwuwar karkatar da kuɗaɗen zuwa harkokin siyasa.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

Ya ƙalubalanci gwamnatin jihar kan dalilin da zai sa a tilasta wa ƙananan hukumomi karɓar wannan babban bashi domin ayyukan da gwamnatin jihar za ta tafiyar da kanta, maimakon barin ciyamomin su tsara abubuwan da suka fi muhimmanci ga yankunansu da kuma amfani da kason kuɗaɗen da suke karɓa daga asusun tarayya.

Haka kuma, ƙungiyar ta buƙaci a fitar da cikakken lissafin kuɗaɗen da ƙananan hukumomin suka bayar a can baya a ƙarƙashin shirin haɗin gwiwa na tallafa wa mata na wata-wata, wanda aka dakatar bai kai wata goma yana aiki ba.

Ta gargaɗi cewa bai kamata a tilasta wa wani shugaban ƙaramar hukuma sanya hannu a kan wani nauyin bashi mai girman gaske ba tare da ya fahimci dukkan ƙa’idojin shari’a da illar da hakan zai haifar ga tattalin arziƙin al’ummarsa ba.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
  • Abubakar Sulaiman
    Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC
  • Abubakar Sulaiman
    Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

MASU ALAKA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna
Manyan Labarai

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai
Manyan Labarai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume
Manyan Labarai

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Next Post
APC Ta Naɗa ‘SSA Media’ Ta Gwamna Mai Goyon Bayan Atiku A Kwamitin Yaƙin Zaɓen Tinubu/Abba

APC Ta Naɗa ‘SSA Media’ Ta Gwamna Mai Goyon Bayan Atiku A Kwamitin Yaƙin Zaɓen Tinubu/Abba

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

October 24, 2026
EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

October 24, 2026
Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

October 24, 2026
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.