Matashiya Khadijah Aminu Shariff, wadda ta bayyana goyon bayanta ga Atiku Abubakar na ADC a zaɓen 2027, na cikin waɗanda aka naɗa a kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Shigar sunan Khadijah Aminu Shariff cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a Kano ta jawo tambayoyi kan matsayinta na siyasa, la’akari da sanarwar da ta fitar a baya tana bayyana goyon bayanta ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukan sada zumunta ranar 24 ga Satumba, 2026, Khadijah ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Atiku, tare da alƙawarin zaɓensa da kuma yin kamfen a madadinsa a babban zaɓen 2027.
A sanarwar mai taken “Sanarwa Ta Musamman”, ta ce ta kuduri aniyar bayar da cikakken goyon baya ga yaƙin neman zaɓen Atiku, tana mai bayyana hakan a matsayin gudummawarta ga harkokin siyasa da tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya.
Khadijah, wadda aka bayyana a matsayin Mataimakiya ta Musamman ga Gwamnan Kano kan kafafen sada zumunta, ta kuma wallafa bidiyoyin da suka shafi ayyukan siyasa na Atiku, ciki har da ziyarar da ya kai Akure domin maraba da wasu ’yan siyasa da suka sauya sheƙa daga jam’iyyun APC da PDP.
Sai dai, an sake mayar da hankali kan matsayinta na siyasa bayan da sunanta ya bayyana cikin jerin mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a Kano, wanda aka fitar ranar 19 ga Oktoba, 2026.
Jerin sunayen ya nuna cewa an ba ta muƙamin Mataimakiyar Darakta ta Uku mai kula da kafafen sadarwa na zamani da kirkire-kirkire (Assistant Director III, Digital Media and Innovation).
Naɗin nata ya jawo tambayoyi kan matsayinta na siyasa, kasancewar ta bayyana goyon bayanta ga Atiku, yayin da kuma aka saka ta cikin kwamitin da zai yi wa Tinubu da Gwamna Abba kamfen gabanin zaɓen 2027.
Kafin bayyana goyon bayanta ga Atiku, Khadijah ta kasance tana amfani da kafafen sada zumunta wajen kare manufofi da ayyukan gwamnatin Kano.
Sai dai, babu wata sanarwa da aka ambata da ke nuna cewa ta janye goyon bayanta ga Atiku ko kuma ta yi ƙarin bayani kan matsayinta na siyasa bayan shigar sunanta cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC.
A wani ɓangare kuma, wasu matasa masu alaƙa da APC sun nuna damuwa kan yadda ake raba muƙaman siyasa a gwamnati. Sun bayyana ra’ayin cewa ya kamata a yi la’akari da gudummawar da mambobin jam’iyya da masu fafutukar siyasa suka bayar wajen samun nasarar jam’iyyar.
Sun kuma yi kira da a tabbatar da adalci wajen raba muƙamai, tare da la’akari da gudummawar da maza da mata suka bayar wajen kafa jam’iyya da kuma nasarar gwamnatinta.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana ko Khadijah ta janye goyon bayanta ga Atiku ba, ko kuma shugabannin APC a Kano sun yi wani ƙarin bayani kan shigar sunanta cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen.
Me kuke ganin wannan naɗi ke nufi ga siyasar Kano da babban zaɓen 2027?














