Hukumomin tsaro a jihohi da dama sun ƙara tsaurara matakan kariya bayan wani gargaɗin tsaro da Rundunar ’Yansandan Nijeriya ta fitar. Gargaɗin, wanda aka aika wa sassan rundunar a ranar 13 ga Satumba, 2026, ya yi nuni da yiwuwar hare-haren haɗin gwiwa kan makarantu, da wuraren ibada, da sansanonin hora na NYSC da sauran wuraren da ba su da cikakken tsaro. Ya kuma buƙaci a ƙarfafa sa ido a yankunan Arewa maso Gabas, da Arewa maso Yamma, da Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Yamma.
A Jihar Katsina, gwamnati ta amince da ɗaukar ƙarin jami’an sa-kai 708 domin kare makarantun gwamnati, musamman waɗanda ke yankunan da ke fama da matsalar tsaro. Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare, Yusuf Sulaiman Jibia, ya ce an kuma umarci makarantu su kafa kwamitocin tsaro, tare da tura ƴansandan tafi-da-gidanka zuwa makarantun kwana da ke cikin haɗari. Rundunar ƴansandan jihar ta ce ta ƙara sintiri da sa ido, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da shugabannin al’umma.
A Binuwai, ƴansanda sun ƙara sa ido da kai sumame a wuraren da ake fama da matsalar tsaro, tare da tura jami’ai zuwa makarantu da sansanonin ’yan gudun hijira. A Kwara kuma, an haɗa rundunar soji, da ƴansanda, da DSS da NSCDC cikin tsarin tsaro na bai ɗaya, yayin da aka ƙara jami’ai a yankunan kudancin jihar da kan iyakar Kogi. Gwamnatocin Neja, da Filato, da Osun, da Oyo, da Ekiti, da Delta, da Imo da Akwa Ibom su ma sun ɗauki matakai daban-daban na ƙarfafa tsaro da sa ido.
Ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta yi kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki gargaɗin da muhimmanci, tare da ɗaukar matakan rigakafi kafin aukuwar wani hari. Sakataren yaɗa labaran ƙungiyar na ƙasa, Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya kuma buƙaci ƴan ƙasa su kasance masu sanya ido tare da kai rahoton duk wani motsi ko mutum da ake zargi ga hukumomin tsaro.














