Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa ba zai halarci taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) karo na uku a jere ba. Atiku ya ce Tinubu bai halarci tarukan UNGA na shekarun 2024 da 2025 ba, inda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilce shi a duka lokutan.
Kalaman Atiku sun biyo bayan sanarwar Fadar Shugaban Ƙasa cewa Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya zuwa taron UNGA karo na 81 da za a gudanar a New York ta Amurka. Ana sa ran Shettima zai gabatar da jawabin Nijeriya tare da halartar tarukan diflomasiyya da ganawa da shugabannin ƙasashe da sauran manyan jami’ai.
Atiku ya ce duk da cewa Shettima zai iya wakiltar Nijeriya, halartar mataimakin shugaban ƙasa ba zai maye gurbin kasancewar shugaban ƙasa da kansa a irin wannan babban taron diflomasiyya ba. Ya kuma ce taron UNGA na samar da damar shugabannin ƙasashe su tattauna batutuwan kasuwanci, da tsaro, da zuba jari da ci gaba da shugabannin sauran ƙasashe.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma tambayi ko wasu batutuwan da suka shafi tarihin Tinubu a Amurka suna da alaƙa da rashin halartarsa taron. Sai dai Atiku ya jaddada cewa ba ya cewa akwai wata doka da ta hana Tinubu shiga Amurka. Ya buƙaci Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana ko akwai wani dalili na doka, ko diflomasiyya, ko rashin lafiya ko na ƙashin kansa da ya hana shugaban halartar taron.
Sai dai, Fadar Shugaban Ƙasa ta ce babu wata matsalar da ta hana Tinubu tafiya Amurka. Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin waje da ƙa’idojin diflomasiyya, Ademola Osodi, ya ce rashin halartar shugaban ba zai rage matsayin Nijeriya a harkokin diflomasiyya ba.
Haka kuma, Jakadan Nijeriya na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce Nijeriya za ta ci gaba da samun cikakken wakilci a taron, yayin da Shettima zai jagoranci tawagar ƙasar.














