ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

by Muhammad
2 months ago

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya raba filaye 1,540 tare da tallafin kuɗi na Naira miliyan 100 ga shugabannin Ƙungiyar masu kula da Rumfunan Zaɓe na Jam’iyyar APC, wadda aka fi sani da ’Yan Akwati, a wani mataki na ƙarfafa tsarin jam’iyyar a matakin rumfunan zaɓe gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba.

Gwamna Yusuf ya bayyana tallafin ne yayin ƙaddamar da ƙungiyar ta ’Yan Akwati a hukumance, inda ya bayyana cewa tsarin rumfunan zaɓe shi ne ginshiƙin nasarar jam’iyyar APC a zaɓe.

ADVERTISEMENT

Ya ce ƙarfafa magoya bayan jam’iyyar a matakin ƙasa zai taimaka wajen inganta wayar da kan jama’a da tattara ƙuri’u, tare da tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wa’adin mulkinsa na biyu, da kuma sauran ’yan takarar APC a zaɓuɓɓuka masu zuwa.

Gwamnan ya ƙara da cewa sake zaɓen Shugaba Tinubu zai tabbatar da ci gaba da aiwatar da sauye-sauye a fannin tattalin arziki da shirye-shiryen bunƙasa ƙasa da gwamnatin tarayya ta fara.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

A cewarsa, rabon filayen da kuma tallafin Naira miliyan 100 an yi su ne domin ƙara wa mambobin ƙungiyar ƙwarin gwiwa, tare da ba su damar gudanar da ayyukan jam’iyya yadda ya kamata a matakin rumfunan zaɓe.

Tun da farko, Mai Bai Wa Gwamna Shawara kan Harkokin Siyasa, Mustapha Hamza Buhari Bakwana, ya bayyana cewa wannan tallafi shi ne kashi na farko kuma wani babban shiri da gwamnatin ke aiwatarwa domin ƙarfafa guiwar jam’iyyar APC a faɗin jihar kafin zaɓen 2027.

Ya bayyana kwarin guiwar cewa ƙungiyar ’Yan Akwati na da shirin tattara sama da ƙuri’u miliyan ɗaya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Jihar Kano.

Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, da wakilan ƙungiyar daga dukkan ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin "Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu"

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.