Daraktan Janar na ƙungiyar City Boy Movement, Francis Shoga, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ɗan takarar da ya fi dacewa ya ci gaba da jagorantar Nijeriya bayan shekarar 2027.
Shoga ya ce gwamnatin Tinubu ta samu ci gaba a ɓangarorin gine-ginen ababen more rayuwa, noma, makamashi da kuma sauye-sauyen tattalin arziƙi.
Ya ambaci manyan ayyuka da suka haɗa da babbar hanyar Legas zuwa Calabar, hanyar Sakkwato zuwa Badagry, da kuma shirin gwamnati na samar da kayan aikin noma domin bunƙasa noma a ƙasar.
Ƙungiyar City Boy Movement, wadda ke goyon bayan Tinubu, ta ce za ta ci gaba da neman goyon bayan matasa domin samun nasarar Shugaban a zaɓen shekarar 2027.














