ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Majalisar Malamai Ta Ƙasa Ta Buƙaci Gwamnati Ta Yi Wa El-Rufai Da Sheikh Sani Zaria Adalci

by Shehu Yahaya
2 days ago
Malamai

Majalisar Ƙoli ta Malamai ta Ƙasa ta yi kira da a yi adalci wajen gudanar da shari’o’in da suka shafi tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da Sheikh Sani Abdulkadir Zaria da sauran waɗanda ake tuhuma, tana mai jaddada muhimmancin bin doka da kare haƙƙin kowane ɗan Nijeriya.

Majalisar ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar da ta fitar bayan taronta na shekara-shekara da aka gudanar a hedikwatar Jama’atu Nasril Islam (JNI), da ke Kawo, Kaduna Wanda Sheikh Ahmed Maqari ya sanyawa hannu.

Ta bayyana cewa ya kamata hukumomin shari’a su tabbatar da adalci ba tare da nuna son kai ba, tare da bai wa duk wanda ake tuhuma damar kare kansa bisa tanadin doka.

ADVERTISEMENT

Majalisar ta kuma jaddada cewa bai kamata a hukunta mutum ba kafin a kammala shari’arsa bisa ƙa’ida, tana mai kira ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa da su mutunta tsarin shari’a da kauce wa duk wani abu da zai iya kawo cikas ga gudanar da adalci.

A cikin sanarwar, Majalisar ta kuma yi kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen magance matsalolin tsaro, tsadar rayuwa da sauran ƙalubalen da ke addabar al’umma.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

Haka kuma, ta yi gargaɗi ga ’yan siyasa da magoya bayansu da su guji kalaman da za su iya tayar da rikici, musamman yayin da ƙasar ke tunkarar babban zaɓen 2027.

Majalisar ta buƙaci gwamnati da al’umma su ba da fifiko ga zaman lafiya, adalci, mutunta juna da bin doka, tare da tabbatar da cewa an kare haƙƙin kowane ɗan Nijeriya ba tare da la’akari da matsayinsa ba.

Malamai
Shehu Yahaya
+ postsBio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Kotu Ta Ba Da Belin Ƴar Jarida Farida Isiak Bayan Tsare Ta A Kaduna
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    NAPTIP Ta Buƙaci ‘Yan Jarida Su Ƙara Bincike Wajen Bayar Da Rahotannin Cin Zarafin Mata
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Kwalejin Koyar Da Ƙwararrun Ma’aikatan Jinya A Rigasa
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    2027: Kaddamar da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna Alamar Nasarar Tinubu Ce A 2027 —Kakakin APC

MASU ALAKA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna
Manyan Labarai

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai
Manyan Labarai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume
Manyan Labarai

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Next Post
Kafofin Yada Labarai Da Dama Na Kasashen Afirka Sun Ziyarci Hunan Don Ganin Ci Gaban Sin

Kafofin Yada Labarai Da Dama Na Kasashen Afirka Sun Ziyarci Hunan Don Ganin Ci Gaban Sin

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

October 24, 2026
EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

October 24, 2026
Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

October 24, 2026
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.