ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rikicin Cikin Gida Ya Ɓarke A Jam’iyyar APM, Wani Ɓangare Ya Tsige Shugaban Jam’iyyar A Bauchi

by Khalid Idris Doya
3 days ago

Wani sabon rikicin shugabanci ya ɓarke a reshen Jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) na Jihar Bauchi, yayin da wani ɓangare na jam’iyyar ya sanar da tsige shugaban jam’iyyar na jihar, Auwal Isah, bisa zargin saɓa wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar da rashin amincewa da salon jagorancinsa.

Sakataren wannan ɓangare na jam’iyyar, Mohammed Nasir Yahaya, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar tare da wasu shugabannin jam’iyyar a ranar Laraba. Ya ce sun kuma amince da naɗa Hon. Nasiru Nuru Marafa a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar a jihar.

Yahaya ya ce rikicin ya samo asali ne bayan sauya shekar Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, da wasu jami’an gwamnati zuwa APM, lamarin da ya haifar da saɓani kan yadda za a raba muƙaman shugabancin jam’iyyar tsakanin tsofaffin mambobi da sababbin waɗanda suka shigo.

ADVERTISEMENT

Ya yi zargin cewa Isah, wanda ya jagoranci jam’iyyar tun shekarar 2018, ya sauya sunayen mambobin kwamitin zartarwa na jiha tare da shigar da wasu mutanen da ya ce ba sa cikin tsofaffin mambobin jam’iyyar, sai dai masu biyayya ga gwamnatin jihar da wasu ɓangarorin PDP.

Ya kuma zargi shugabancin jam’iyyar da amincewa da tsarin da zai bai wa gwamnatin jihar kashi 70 cikin 100 na muƙaman shugabanci, yayin da tsofaffin mambobin za su riƙe kashi 30 cikin 100.

LABARAI MASU NASABA

Me Tinubu Zai Yi Wa Arewa Alƙawari A Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓensa A Kaduna?

MDPCO Ta Soki Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Kaduna

A cewarsa, an kafa kwamitin sasanci domin warware saɓanin, amma an dakatar da ayyukansa bayan kwanaki huɗu. Ya ce duk da miƙa ƙorafe-ƙorafe ga shugabancin jam’iyyar na ƙasa da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ba a warware matsalar ba.

Yahaya ya ƙara da cewa sun sanar da INEC da shugabancin jam’iyyar na ƙasa a hukumance kan matakin tsige Isah. Ya kuma ce Gwamna Bala Mohammed ya buƙaci ɓangarorin da ke rikicin da su kiyaye zaman lafiya domin hana matsalar ta’azzara.

Sai dai wani ɓangare na jam’iyyar ya yi watsi da sanarwar tsige shugaban.

Sakataren yaɗa labaransa, Abdulshakur Danlami Mohammed, ya ƙalubalanci iƙirarin Yahaya na cewa shi ne sakataren jam’iyyar, yana mai cewa ba shi ne sakataren da jam’iyyar ta amince da shi ba.

Ko da yake bai musanta cewa waɗanda suka nuna rashin amincewa da Isah mambobin jam’iyyar ba ne, Mohammed ya ce za su mayar da martani yadda ya dace kan lamarin.

Khalid Idris Doya
+ postsBio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    2027: Mazauna Bauchi Sun Ƙalubalanci Iƙirarin Limami Na Cewa An Cire Shi Saboda Tallar Tinubu
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Kakakin Majalisar Bauchi Ya Tsallake Rijiya Da Baya Yayin Da Tawagarsa Ta Gamu Da Hatsari

MASU ALAKA

Tinubu Ya Ce Ba Zai Iya Raka ‘Yan Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa Kowace Jiha Ba
Siyasa

Me Tinubu Zai Yi Wa Arewa Alƙawari A Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓensa A Kaduna?

October 24, 2026
MDPCO Ta Soki Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Kaduna
Siyasa

MDPCO Ta Soki Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Kaduna

October 24, 2026
Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’
Siyasa

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

October 23, 2026
Next Post
Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Ɗan Majalisa Na Watanni 3 Kan Fitar Bidiyon Jan Kunnen Zomo

Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Ɗan Majalisa Na Watanni 3 Kan Fitar Bidiyon Jan Kunnen Zomo

LABARAI MASU NASABA

Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Sun Haifar Da Yunwa Da Talauci A Nijeriya, Muna Ƙoƙarin Kawar Da Su – Tinubu

Sun Haifar Da Yunwa Da Talauci A Nijeriya, Muna Ƙoƙarin Kawar Da Su – Tinubu

October 24, 2026
Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

October 24, 2026
Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci

Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci

October 24, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC

Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC

October 24, 2026
Hukumar Zaɓe Ta Wayar Da Kan Nakasassu Kan Kaɗa Ƙuri’a A Zamfara

Hukumar Zaɓe Ta Wayar Da Kan Nakasassu Kan Kaɗa Ƙuri’a A Zamfara

October 24, 2026
Tinubu Ya Ce Ba Zai Iya Raka ‘Yan Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa Kowace Jiha Ba

Me Tinubu Zai Yi Wa Arewa Alƙawari A Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓensa A Kaduna?

October 24, 2026
Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

October 24, 2026
Magoya Bayan ‘Tinubu Must Come’ Da ‘Tinubu Must Go’ Sun Yi Arangama

Magoya Bayan ‘Tinubu Must Come’ Da ‘Tinubu Must Go’ Sun Yi Arangama

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.