ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NDLEA Ta Kama Ƙwayar Tiramadol 396,000 A Filin Jirgin Saman Yola

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
4 weeks ago
NDLEA

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) sun kama kwantena 396,000 na Kwayar tramadol a Filin Jirgin Sama na Aliyu Mustapha, Yola.

Wannan sabon kamen ya zo ne kasa da sati guda bayan hukumar ta samu fiye da kwantena 171,000 ta tramadol a lokacin wasu ayyukan daban a jihohin Neja, Binuwe, da Taraba.

  • Akwai Bukatar Karfafa Hadaka Domin Ciyar Da Tashoshin Jiragen Ruwa Gaba A Afirka —Dantsoho
  • Gwamnan Neja Ya Yi Allah-Wadai Da Sace Ɗaliban St. Mary A Papiri

A cikin sanarwa da aka fitar, kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana cewa wani mutum mai shekaru 50, Ahmed Nda, an kama shi akan wannan laifi.

ADVERTISEMENT

A cewar sanarwar, “A Jihar Adamawa, jami’an NDLEA sun samu kwantena 396,000 ta kwayar tramadol daga hannun wani mutum, Ahmed Isyaku Nda, mai shekaru 50, a Filin Jirgin Sama na Aliyu Mustapha, Yola, yayin da aka samu kilo 785 na skunk a cikin ma’ajiyar wani mai sayar da kwayoyi da ke gudun hijira a Asob Maraba Karu, Jihar Nasarawa.”

A wani labari mai alaka, Babafemi ya tabbatar da kama wani babban mai safarar kwayoyi da ake nema wanda ya yi basaja a matsayin mai aiki a karkashin kasuwanci da Otal.

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa Uku Bayan Rufe Makarantu A Adamawa

Sojoji Sun Kama Babban Mai Sayar Da Miyagun Kwayoyi Ga ‘Yan Ta’adda Na Boko Haram

“Wannan mutum mai shekaru 42, Ibemesi, wanda shi ne MD/CEO na Franc CJ Ibemesi Nig. Ltd, an kama shi a otal dinsa na Daisy Garden Hotel, 66–68 Agbeke Street, Ago Palace Way, Isolo, Lagos, da sassafe.”

“Daga bisani an kai shi zuwa ma’ajiyarsa a 7 Pius Ezeobi Street, Off Ago Palace Way, Isolo, inda aka samu jakunkuna 42 manya da kwalaye hudu na Loud, wani nau’in tabar wiwi, da nauyin kilo 1,762.8.

“Haka kuma, an kwato Dala 11,600, da Fam 2,000 na Birtaniya, da Euro 2,200, da Dalar Kanada 50, duka a cikin kudi na hannu,” in ji Babafemi.

Har ila yau, ya bayyana cewa an tarwatsa yunkurin wata kungiyar safarar kwayoyi da ke aiki daga dajin Orita-Apeje, Araromi-Okeodo a Karamar Hukumar Ife ta Kudu, Jihar Osun, na rarraba kilo 11,135 na skunk da aka sarrafa, bayan kwanaki na leken asiri.

A cewarsa, “An kwato motoci biyu da ake amfani da su wajen safarar kayan haramtacciyar — mota Bolbo mai lambar WWR 29 DA da mota Mercedes mai lambar rajista AWK 713 YZ — sannan an kama mutum bakwai.”

Mutanen da ke hannun hukumar, a cewar Babafemi, sun hada da Lucky Abiodun, Julius Amos, Bictor Ngbikili, Sunday Oduegwu, Ibrahim Akanni, Eze Godstime, da Fred Ifeanyichukwu.

Yayin yabawa da jami’an da suka shiga cikin ayyukan daban-daban, Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya yi kira ga duk ma’aikatan a fadin kasar da su ci gaba da bin tsarin kula da kwayoyi na hukumar daidai da hadin kai.

Wani rahoto daga PUNCH Metro ranar Talata ya bayyana wani sabon aikin leken asiri inda NDLEA ta kwato haramtattun kayan da ke da darajar kimanin Naira biliyan 338 a tashar PTML ta Tin Can Island Port a Legas.

Hukumar ta ce tana yin hadin gwiwa da US DEA da National Crime Agency ta Birtaniya domin gano wadanda ke da alhakin wannan kaya.

A wani labari mai alaka da wannan, Babafemi ya tabbatar da kama wani babban mai safarar kwayoyi da ake nema wanda ya yi basaja a matsayin dan kasuwa da ke zaune a wani Otal

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi
Tsaro

‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa Uku Bayan Rufe Makarantu A Adamawa

November 29, 2025
Wani Mai Taɓin Ƙwaƙwalwa Ya Kashe Soja A Legas
Tsaro

Sojoji Sun Kama Babban Mai Sayar Da Miyagun Kwayoyi Ga ‘Yan Ta’adda Na Boko Haram

November 21, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas
Tsaro

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Next Post
Firaministan Sin Ya Ce A Shirye Yake Ya Yi Aiki Da Zambiya Da Tanzaniya Wajen Gina Sabuwar Cibiyar Tattalin Arziki

Firaministan Sin Ya Ce A Shirye Yake Ya Yi Aiki Da Zambiya Da Tanzaniya Wajen Gina Sabuwar Cibiyar Tattalin Arziki

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.