Bayan kasa da awanni 24 da gwamnatin Jihar Adamawa ta rufe makarantun kwana, ‘yansanda sun kama masu satar mutane uku a jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar a Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa kamun ya biyo bayan korafi da aka samu a ranar 19 ga Nuwamba, 2025, daga wani mazaunin wani kauye a Karamar Hukumar Song, cewa a ranar 18 ga Nuwamba, 2025, ya samu kiran waya ta barazana daga wani da ba a san ko waye ba.
- Dogaro Da Noman Gargajiya Kadai Ba Zai Iya Wadatar Da Nijeriya Ba – Farfesa Rabi’u
- Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
A cewar sanarwar, mai kiran waya ya nemi a biya shi Naira miliyan 2 ko kuma a yi garkuwa da shi har ma da yiwuwar a kashe shi.
“Bayan karbar korafin, kwamishinan ‘yansanda, Dankombo Morris, ya umurci Mataimakin Kwamishinan ‘Yansanda na Sashen Bincike na Jiha, Yola, da ya gudanar da bincike tare da tabbatar da kama masu laifin,” in ji shi.
Mutanen da aka kama su ne Ahmadu Alhaji Halilu, mai shekara 24; Adamu Buba Balejo, mai shekara 21; da Hassan Alhaji Liman, duk maza daga Gundumar Malabu a Karamar Hukumar Fufore.
“Yayin binciken, wadannan mutum uku sun amsa laifinsu. An kuma samu katin SIM da aka yi amfani da shi wajen aikata laifin, wanda za a dauka a matsayin hujja.”
Kwamandan ‘yansanda, wanda ya yaba wa jami’an da suka shiga aikin, ya tabbatar da jajircewar rundunar wajen ganowa da kama, da gurfanar da masu laifi a fadin jihar.
Gwamnatin Jihar Adamawa ta rufe dukkan makarantun kwana na gwamnati da masu zaman kansu a jihar a ranar Asabar.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan Ilimi da Ci gaban Dan’Adam, Dr Umar Pella, ya sanyawa hannu, an bayyana cewa matakin Fintiri na rufe makarantun kwana yana nufin kauce wa faruwar irin sace dalibai da aka yi a Jihohin Neja da Kebbi.
“Dangane da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a yanzu, musamman abin da ya faru da dalibai a Jihohin Neja da Kebbi, an lura da takaici cewa makasudin masu laifi su ne makarantun sakandire na kwana.
“Idan aka yi la’akari da wannan mummunan yanayi a kasar, Mai Girma Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya umarce ni da in rufe dukkan makarantun kwana a fadin jihar, ko makarantu na gwamnati ne ko masu zaman kansu.”
Ya kara da cewa, “Dukansu su kasance makarantun jeka da ka dawo a halin yanzu. Saboda haka, ta wannan wasika, dukkan shugabanni da masu mallakar makarantu na gwamnati da na masu zaman kansu su mayar da dalibansu jeka ka dawo.”














