Kungiyar tuntuba na dattawan arewa (ACF) ta shawarci ‘yan Nijeriya su amince da duk wani sakamakon zaben wannan shekara domin farfado da dimokuradiyyar Nijeriya.
A cewar kungiyar, dole ne a samu wadanda suka yi nasara da kuma wadanda suka fadi, inda ta jaddada cewa ko ta yaya aka bi, ka da wani ya yi yunkurin rashin tayar da zaune tsaye ta hanyar tayar da hankulan ‘yan Nijeriya da sakamakon zaben.
- Sin Za Ta Ci Gaba Da Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Warware Rikici Cikin Lumana Ta Hanyarta
- Sin Ta Yi Kira Ga Al’ummar Kasa Da Kasa Da Ta Kara Mai Da Hankali Kan Batun Somaliya
A wata sanarwa da babban sakataren kungiyar, Malam Murtala Aliyu ya fitar, ta ce duk wani yunkuri na kin amincewa da sakamakon zaben, zai zama wani mummunan farmaki ga dimokuradiyyar kasar nan, amincewa da zaben yana daya daga cikin ginshiki na tsarin dimokuradiyya.
Sanarwar ta bayyana cewa, “Kudirin ‘yan Nijeriya na kammala zaben 2023 cikin nasara bai taba shiga cikin shakku ba. Idan aka yi la’akari da duk abin da aka cimma, babu wani dalili da zai sa wani ya yi yunkurin yin kutse ga jadawalin zabe da aka sanar. Wannan ba zai zama abin karba kwata-kwata ba.”
Kungiyar dattawan arewa ta bukaci shugabanni a dukkan matakai da su dauki matakan tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin daukacin ‘yan kasa da na kasashen waje a yankunansu gabanin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe, inda ta ce ‘yan Nijeriya su tabbatar da an samu zaman lafiya da lumana daga gwamnatin farar hula zuwa wata gwamnatin ta farar huda.
Haka kuma kungiyar ta shawarci kafafen yada labarai da su taka rawar gani wajen kawar da duk wani tashin hankali da ka iya tasowa lokacin bayyana sakamakon zabe.
ACF ta bayyana farin cikinta da bullo da fasahar sadarwa a harkar zabe, inda ta jaddada cewa mataki ne da ya dace da zai tabbatar da magance magudin zabe da aka saba a baya da kwace akwatin zabe da kuma sauya sakamakon zabe.
Kungiyar ta yi imanin cewa watsa sakamakon zabe ta yanar gizo daga wuraren zabe zuwa cibiyoyin tattara sakamakon zabe da kuma samar da kayayyakin da mutane za su rika sanya ido kan sakamakon zabe ta yanar gizo abubuwa ne da za su tabbatar da cewa ba a tafka magudi a zaben ba.
Sanarwar ta yaba wa kokarin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) na samar da yanayi mai kyau da zai tabbatar da an gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci, kuma duk kuri’un da aka kada a kasar nan za a kirga.
Kungiyar ta shawarci masu kada kuri’a da su yi la’akari da bayyanannun manufofin jam’iyya da kuma halaye da tarihin ‘yan takara.
Ta shawarci ‘yan Nijeriya da su kada kuri’unsu bisa la’akari da kabilanci, addini ko yanki, inda ta jaddada cewa ya kamata su nemi shugabannin da suka fi dacewa da muradun kasar nan.