ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1

by Nuhu Ubale Ibrahim
2 years ago
Layya

Da sunan Allah mai Rahama mai Jin ƙai. Yabo da godiya da kirari da girmamawa sun tabbata ga Allah Shi kaɗai. Yabon Allah da amincinsa su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta, shugaban na farko da na ƙarshe tare alayensa da sahabbansa baki-ɗaya.

Bayan haka:
Wannan rubutu ya ƙunshi bayani a kan layya a bisa fahimtar Mazhabar Imamu Maliku ɗan Anas, Imamu Daril Hijrati Allah ya ji ƙansa, watau Malikiyya. Na zaɓi rubutun ya zama a haka saboda Mazhabar Malikiyya ake bi a wannan yanki namu, tare da kuma ƙarfin hujjoji da Mazhabar take da shi.

  • Layya Babbar Ibada: Yadda Ake Gudanar Da Ita Da Matsayinta A Musulunci
  • Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 2
  • Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 3

Layya sunna ce mai ƙarfi a Muslunci ga duk wanda ya samu iko, wannan ita ce magana mashahuriya a Malijiyya. Duba; Arrisãlatu [shafi na 107]da Attalƙīnu [shafi na 211] da Alma’ūnatu [1/484] da Addurarul Bahiyyati [shafi na 145] da Al’irshadu [shafi na 100].

ADVERTISEMENT

Wannan sunnar mai ƙarfi ta ƙunshi namiji da mace waɗanda suke ‘ya’ya ba bayi ba. Duba ; Alkãfi [shafi na 236] da Assharhus Sagīr [2/339].

Manya da yara sunna ce mai ƙarfi su yi layya matuƙar suna da ikon yi. Duba Iziyya tare da Fathu Rabbil Bariyyati [shafi na 763] . Kuma yaro ko maraya ne zai iya neman majiɓincin al’amarinsa ya ya yi masa layya matuƙar yana da wadatar yi. Duba; Sharhul Iziyya na Sharnūbi [142].

LABARAI MASU NASABA

Shekara Biyar Da Rasuwar Sam Nda-Isaiah

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3

Saboda haka; layya ba sai mai aure ne yake yi ba, ibada ce mai girman gaske da ɗimbin lada, samari da ‘yan mata da zawarawa da tuzurai za su iya yinta, haka nan macen da take a gidan aure za ta iya yi idan tana da sarari koda kuwa mijinta ya yi, domin neman lada a wurin Allah Ta’ala matuƙar suna da iko. Layya tana daga cikin alamomi (sha’a’ir) na addinin Islama kuma tana da falalar gaske.

Layya ta fi ‘yanta wuya (‘yanta bawa) da sadaƙa falala saboda tana cikin Sha’a’ir na Muslunci. Duba; Aljawãhiruz Zakiyyati [shafi na 143] da Addurarul Bahiyyati [shafi na 145].

Wata Fa’ida: A cikin malaman Malikiyya akwai waɗanda suke ganin layya wajibi ce ga duk mai iko. Kuma wannan magana ita ce shahararren malami kuma ƙwararre a Malikiyya mashahurin malami Farfesa Mansur Sokoto Allah ya zama gatansa ya rinjaryar kuma ya fi ganin ingancin ta. Duba Muhd Mansur Sokoto; Fathu Rabbil Bariyyati [shafi na 767].

Ana layya ne da jinsin dabbobi na ni’ima guda huɗu kamar haka:
1. Tumaki
2. Awaki
3. Shanu
4. Raƙuma.

Mu haɗu a rubuta na 2 don sanin shekarun dabbar da za a yi layya da ita.

Nuhu Ubale Ibrahim
ABU RAZINA PAKI
8/12/1442
Bugu Na 2

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shekara Biyar Da Rasuwar Sam Nda-Isaiah
Bakon Marubuci

Shekara Biyar Da Rasuwar Sam Nda-Isaiah

December 19, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3
Ilimi

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3

December 14, 2025
Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148
Ilimi

Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148

December 14, 2025
Next Post
Zan Iya Yi Wa Mamaci Layya?

Zan Iya Yi Wa Mamaci Layya?

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.