A kokarin dakile yawan kai wa masu sana’ar tsoffin karafa farmakin da mayakan Boko Haram ke yi a jihar Borno, Gwamna Farfesa Babagana Zulum, ya kafa dokar haramta sana’ar a fadin jihar, har sai baba ta gani.
Gwamnatin jihar ta kara da cewa, kafa dokar ya zama dole domin kare rayukan masu sana’ar gwangwan, sakamakon hare-haren da `yan ta’addan Boko Haram ke kai musu a baya-bayan nan.
- Cire Tallafin Mai: Za A Kara Farashin Burodi A Nijeriya
- Kyakkyawar Alakar Sin Da Amurka Fa’ida ce Ga Duniya Baki Daya
A wata sanarwar manema labaru mai dauke da sa-hannun Mallam Isa Gusau, mai magana da yawun Gwamna Zulum, ya ce, “An kafa wannan dokar ce domin dakile farmakin da yan ta’addan Boko Haram ke kai wa masu wannan sana’ar a wasu kananan hukumomi da kuma hana satar dukiyar jama’a da ake yawan samu.”
Gusau ya kara da cewa, hakan ya zo ne sakamakon yadda wasu wadanda ba a san ko su waye ba, suna zuwa kauyukan da yan ta’addan Boko Haram suka tarwatsa, domin neman tsoffin karafa, inda Boko Haram ke yi musu kwanton bauna tare da kashe su.”
A cewar Gwamna Zulum “A cikin shekaru biyar da suka wuce, an kashe mutane da dama a lokacin da suke shiga kauyuka, a sana’ar gwangwan. Hakan ya sanya dole gwamnatin jihar Borno ta dauki matakin bincike kan matsalolin, al’amarin da ya tilasta kafa wannan dokar.” In ji Zulum.
“Sannan kuma a wadannan wuraren, akwai dukiyoyin gwamnati, da na kamfanonin sadarwa. Wanda irin wadannan ayyuka na sana’ar gwangwan ke zama kalubale da kuma zagon kasa ga Gwamnatin Tarayya da na jihar Borno wajen kula da su. Saboda haka na bayar da umarnin hana sana’ar gwangwan ta karafa a dukkan kananan hukumomin jihar Borno 27.”
Bugu da kari, Gwamna Zulum ya bayyana cewa, wadannan masu sana’ar gwangwan sun yi kaurin suna wajen lalata dukiyoyin jama’a da na kamfanoni masu zaman kansu a mafi yawan kananan hukumomin da rikicin Boko Haram ya tilasta wa mazaunansu tserewa.
Gwamna Zulum ya kara da cewa gwamnatin jihar ta yi asarar kadarori na biliyoyin Naira a cikin shekaru biyar da suka gabata sakamakon ayyukan masu sana’ar gwangwan a jihar.
Gwamnan ya ce wannan dokar ta shafi duk wani nau’i na sana’ar tsoffin karafa wanda ba bisa ka’ida ba, wanda ya hada da wargazawa, tarawa, da kuma jigilar tsoffin karafan a fadin jihar.
Gwamna Zulum ya yi gargadin cewa gwamnatin jihar Borno za ta hada gwiwa da jami’an tsaro wajen aiwatar da dokar yadda ya kamata tare da zartar da hukunci mai tsauri ga duk wanda ya karya dokar.