Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa a yanzu haka ‘yan Nijeriya wadanda suka zabi Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu suna nadama.
Shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Ondo, Fatai Adams, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren yada labaran jam’iyyar, Kennedy Peretei da ya fitar birnin Akure.
A cewar jam’iyyar, ‘yan watannin da shugaban ya yi a kan karagar mulki ya kara ingiza ‘yan Nijeriya a cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa da ba a taba ganin irinsa ba.
Adams wanda ke mayar da martani ga shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Ondo, Ade Adetimehin, wanda ya ce jam’iyyar PDP ta fada cikin rudani.
Ya ce a maimakon jam’iyyar APC da gwamnatinta su mayar da hankali kan mawuyacin halin da suka jefa ‘yan Nijeriya a ciki na tsawaon shakara 8 da suka yi a kan karagar mulki, sai suka kama wani abu daban.
A cewarsa, “Kila Adetimehin shi ne kadai mutumin da ya manta da cewa, al’ummar Jihar Ondo suna sane cewa jam’iyyarsa ta APC ita ce silar da ta jefa mutane cikin wannan mawuyacin halin da suke ciki a halin yanzu, musamman ma lokacin da aka cire tallafin mai.
“Bai fahimci lamarin ba, wanda hatta wadanda aka yaudare su su zabi APC a 2023, tuni sun yi nadama tare da kokawa da yadda kuskuransu suka jawo wa kansu da iyalansu wahala.
“Irin wannan mutum idan yana da kunya ya kamata ya durkusa ya roki al’umma kan babbar masifar da jam’iyyarsa ta jefa mutane.
“Har yana iya bude bakinsa ya ce PDP ta mutu, wannan ai abun dariya ne.
Da yake mayar da martani game da sauya shekar ‘ya’yan PDP zuwa jam’iyya mai mulki a jihar, Adams ya ce “Mafi rinjayen kansilolin 203 da Adetimehin ke bikin shiga jam’iyyarsa ba su taka rawar gani ba a zabukan da suka gabata a Jihar Ondo.
“Kadan daga cikinsu sun kasance a APC tun 2016. A bayyana yake yadda suka sauya sheka zuwa PDP haka suka koma APC, amma ba kowa ne zai iya fahimtar ba, musamman Adetimehin da ke shugabantar jam’iyyar APC mai cike da hadari a jihar, ya kamata ya daina yaudarar kansa.
“Jam’iyyar PDP a Jihar Ondo ta rabauta da wasu ‘yan tsiraru da ke cikin halin kaka-ni-ka-yi a cikin jirgin Adetimehin na APC da ya nutse.
“Yayin da muke tausaya wa irin wadannan mutane, abin takaici ne wadanda ya kamata su yi kuka suna rawa da murna.
“Amma ba da dadewa ba, gaskiyar za ta bayyana a kansu cewa lalle sun kasance makarya”.
Shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa PDP ba ta durkushe ba, kuma hakan ba zai taba faruwa ba.