Hukumar bunkasa kiwon lafiya matakin farko ta kasa ta kaddamar ta kwamiti mai zaman kansa, da zai gano matsalolin da suke damuwar asibitoci a fadin Nijeriya.
Babban jami’i kuma shugaban hukumar NPHCDA, Dakta Faisal Shuaib shi ne ya kaddamar da kwamitin a Abuja Babban Birnin Tarayya, ya bayyana cewa gwamnatocin tarayya, Jihohi, da kananan hukumomi sun sa kudade masu yawa a tsarin tafiyar da kula da lafiyar al’umma matakin farko.
- Nnamdi Kanu Ya Maka Gwamnatin Tarayya A Kotun Koli
- Tinubu Ya Bukaci Manyan Masu Kalubalantarsa Atiku Da Obi Da Su Janye Daga Takara
Sai dai kuma duk da kudaden da suka sa har yanzu basu ga wani cigaban azo a gani ba, tunda har yanzu ana samun mutuwar mata masu juna biyu da kananan yara.
Yace “A shekaru biyu da suka gabata an samu cigaba mai gamsarwa, amma shi ma din bai kai ace an yaba ba, bai kuma dace da abinda ya dace mu samu a matsayinmu na kasa.Wannan shi yasa mu yin aiki tare da gidauniyar Dangote da ta Bill da Gate ga kuma ta Gwamnonin.Ga asusun kula da al’amuran gaggawa na kananan yara na majalisar dinkin duniya, Hukumar lafiya ta duniya,Taraiyar Turai, Bankin duniya,ga kungiyar cigaban kasa da kasa ta kasar Amurka.Hakan shi yasa muke ganin zuwa yanzun muna iya yin magana kan cigaban da aka samu, kan wani alkawarin da aka dauka na Seattle domin mun ga irin gudunmawar da Jihohi suka bada dangane da su kananan Asibitoci”.
Faisal yace wannan shi ne dalilin da yasa suka kasance cikin murna da jin dadi a Hukumar ta kula da lafiya matakin farko ta kasa, ma’aikatar lafiya ta Tarayya da sauran ‘yan kwamitin kulawa suna da mashahuran ‘yan Nijeriya daga Malaman manyan makarantu kan taimakon da suke yi ma al’umma.Ya kara jaddada cewa hukumar tana jiran tayi aiki da kwamitin domin kara bunkasa ayyukan wuraren kula da lafiyar al’umma matakin farko.
Da take jawabi lokacin kaddamarwa jami’a, mai wakiltar ofishin asusun kula da al’amuran gaggawa na kananan yara na majalisar dinkin duniya na Nijeriya, Cristian Munduate ta nuna jin dadinta a kasance cikin wadanda za ayi abinda zai zama tarihi, na kokarin da ake na kara inganta kulawa da lafiyar al’umma,a karkashin Kudurin da aka cimmawa a zaman taron na Seatle.
Ta ce taron ya cimma dukkan sharuddan da suka kamata shi yasa ma kwamitin da zai lura da bada shawara kai tsaye da yin bayani kan kokarin da kowacce Jiha tayi, domin tabbatar da shi tsarin da aka yi kudurin amfani da shi, ya kasance akwai adalci, rikon amana, da kasancewa ko wanne lokaci aka bukaci sanin halin da ake ciki babu wani bata lokaci za a sani.
“Ta kara jan hankali wajen bayyana yadda hukuma UNICEF ta jajirce da ganin sai an aiwatar da duk matakan da aka dauka lokacin da aka yi taro a Legas dangane da matsalolin da ake fuskanta.Yana da kyau a tuna dacewa dukkan gwamnonin Jihohi 36 sun samu halartar taron da kansu, domin nuna a shirye suke su bada duk gudun mawar da ake son su bada don a cimma burin abinda aka sa gaba”.
Bugu da kari tace UNICEF a shirye take ta hada kai da Nijeriya da duk sauran wadanda ake tafiya tare domin tabbatarwa ‘yan Nijeriya suna samun dukkan abubuwan da suke bukata, na kula da lafiyarsu kamar yadda ya kamata, ba tare da shan wahalar yadda za a samu abin yin amfani wajen neman kula da lafiyar.
Shi ma Babban darekta na kungiyar gwamnoni ta Nijeriya Mista Asishana Okauru cewa yayi kungiyar bata siyasa bace, amma tana yin taro aklai- akai domin tattauna al’amuran da tsare- tsaren da suka shafi abubuwan kawo cigaban al’umma.
Yace shi kwamitin mai zaman kan da aka kaddamar zai iya gano Jihohi da gwamnonin wadanda suka kasa cimma abubuwan da aka amince da ayi hakan, ya gode masu mabobin kwamitin mai zaman kansa wajen amincewar da suka yi na aiki tare da kungiyar gwamnaoni ta Nijeriya.
“Hakanan ma a shekarar 2016 Shugabannin kungiyar an karbi bakuncinsu a Ciato wanda gidauniyarby the Bill-gate da Dangote ,wanda daga karshe aka samu wata matsaya da ake kira da suna yarjewar Ciato. Babban abinda suka sa gaba shi ne hanyar da za ayi amfani da ita domin tabbatar da duk kudurorin an samu cim masu kamar dai yadda ya bayyana”.
Akauru yace akwai wata tawaga ta wasu kwararru mai zaman kanta wadda zata rika taimakawa wajen tabbatar da duk abubuwan da aka amince za ayi ana aiwatar dasu, sai dai manufa ita ce ana son su yi aikinsu na kwararru ba su sa kansu cikin siyasa ba, shi yasa ma suka hada kungiyoyin biyu domin aiki tare.
A nata jawabin shugabar kungiyar mai zaman kanta da zata rika sa ido kan yadda ake aiwatar da tsare- tsaren Farfesa Florence Ejembi cewa tayi babbar rana ce,domin tun lokacin Ministan lafiya Farfesa Ransom Kuti tun, a shekarar 1986,inda aka fara daukar matakai na kawo gyara a harkar kula da lafiya, wani mataki nha kula da lafiyar al’umma bai daya bangaren mataki na farko.