Jam’iyyar ADC a Jihar Jigawa ta nuna rashin amincewa da cire sunan Aminu Ibrahim Ringim, wanda ta ce ta miƙa a matsayin mataimakin ɗan takararta na gwamna, daga jerin sunayen ’yan takarar zaɓen 2027 da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar. Maimakon sunansa, hukumar ta saka Musa Ya’u Balarabe a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar, Sabo Muhammad Nakudu.
Mataimakin Shugaban ADC na Jihar Jigawa, Nuraddeen Jidawa, ya tabbatar da cire sunan Ringim a wata hira da jaridar Punch ta yi da shi ta wayar tarho ranar Lahadi. Ya kuma bayyana cewa sunayen wasu ’yan takara kusan bakwai da jam’iyyar ta amince da su, waɗanda ta ce ta miƙa wa INEC bisa ƙa’ida, su ma ba su bayyana a jerin ba.
Jidawa ya ce a matsayinta na jam’iyya, ADC na ci gaba da ɗaukar Ringim a matsayin wanda ta miƙa a hukumance domin ya zama mataimakin ɗan takararta na gwamna. Ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta ɗauki jerin da INEC ta fitar a matsayin wanda za ta amince da shi ba tare da ƙalubalantar hakan ba, yana mai cewa za ta ci gaba da tuntuɓar hukumar ta hanyoyin da doka ta amince da su. Ya zargi lamarin da zama yunƙurin kawo cikas ga jam’iyyar a Jigawa da sauran sassan ƙasar.
Ya ƙara da cewa sauran ƴan takarar da abin ya shafa sun haɗa da waɗanda za su fafata a mazaɓun tarayya da jihohi, ciki har da Hadejia/Auyo/Kafin Hausa, Kaugama da Birnin Kudu. Jidawa ya buƙaci ’yan jam’iyyar da magoya bayanta su kwantar da hankalinsu, yana mai fatan za a warware matsalar ta hanyar kotu bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar da Dokar Zaɓe.
Sai dai Adamu Sawaba, shugaban sashin wayar da kan masu zaɓe da yaɗa bayanai na INEC a Jigawa, ya ce jerin da hukumar ta manna a shalƙwatar ranar Asabar shi ne na ƙarshe.
Ya tabbatar da cewa sun samu koke-koke kan sunayen wasu ƴan takara, amma ya ce duk wanda bai gamsu ba zai iya neman haƙƙinsa a kotu, domin INEC ba za ta sauya sunaye ba sai bisa hukuncin kotu.
Ya kuma nuna cewa matsalar na iya kasancewa da alaƙa da rajistar kasancewa mamba a jam’iyya kamar yadda Dokar Zaɓe ta tanada.














