ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Za Ka  Kare Kanka  Daga Masu Kwacen Facebook  Da  WhatsApp (I)

by Ibrahim Sabo
4 years ago
Facebook

A kwanan nan kwacen shafin sa da zumunta na Facebook da WhatsApp, wanda a turance ake kira ‘Hacking’ ya zama ruwan dare, mafi yawan mutane sun rasa ta yaya hakan yake faruwa.

Duk da mun yi bayanin a baya, to kasantuwar yadda abin ya sake dawo wa, to shi ne yanzu za mu dan yi bayanin yadda mutum zai kare kansa daga fada wa tarkon wadannan masu kutsen.

  • Tsegunta Barazanar Tsaro Daga Ofishin Jakadancin Amurka: Wa Abin Zai Amfanar?
  • An Fara Rangadin Nuna Kashi Na Uku Na Fina-Finan Kasar Sin A Afirka

Bari mu fara da Whatsapp, wanda mutane da yawa suke mamakin, wasu mutanen kuma suke ganin kamar ba zai yi yu a kwace shi ba, saboda lambar waya kadai ake amfani da shi wajen budewa kuma mafi yawan mutane ba su damu da yin hira ‘chatting’ da mutanen da ba su san su ba a WhatsApp din.

ADVERTISEMENT

Wasu har sukan iya cewa ma ta ina Bature zai samu lambar su har ya iya kwace musu WhatsApp din? Shin ta yaya ma zai fara? Da dai wasu tunani da suka dogara da su na kin yarda ana iya kwacewa.

Duk da cewa yanzu an fara ganin zahiri cewa ana iya ‘Hacking’ din  WhatsApp din,  kuma wasu ma an musu, to wane mataki ya kamata a dauka dan ganin an dakile faruwar hakan nan gaba?

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

Hanya mafi sauki da za ka bi don dakile yi maka kutse a WhatsApp dinka shi ne, ka shiga ‘SETTING ‘ a cikin WhatsApp din naka, sai ka shiga ‘TWO STEP BERIFICATION’ ka saka shi.

Yaya ake saka two step berification a WhatsApp?

Idan ka shiga ‘settings’ ka duba ‘account settings’ a ciki za ka ga ‘Two Step Berification’ sai ka shiga ka saka abin da suka tambaya, sannan kuma za su bukaci ka saka Email dinka domin toshe duk wani yunkuri na yi maka kutse a WhatsApp dinka.

Ta Yaya Za Ka Kare Kanka Daga Masu Kwace Shafin Facebook?

Mafi yawan mutane idan sun bude shafi a sahar Facebook ba sa la’akari da seta wasu abubuwan, musamman wadanda suka shafi layin tsaro kamar boye wasu muhimman sirruka game da mutum kansa.

Wasu daga cikin mutane idan sun bude shafin Facebook, sukan yi amfani da makullan sirri mafi sauki ta yadda ba za su taba mantawa ba, mafi rinjaye daga cikin su, suna amfani da lambobin wayar su lambar kuma wanda suka riga suka yi rijista wajen bude shafin Facebook din da ita.

Shin laifi ne amfani da lambar waya a matsayin makullin sirri ‘password’?  A’a ba laifi ba ne amma akwai bukatar boye lambar wayar daga masu bude ko bincika shafin ‘profile’ din mutane don ganin sirrukansu ko samun lambobin su.

Yana da matukar muhimmanci mu san cewa masu kutse cikin shafin mutane na Facebook, mafi yawa daga cikin su ta hanya mafi sauki suke iya shiga, shi ne rashin tsaro da kuma rashin ba da muhimmancin da muke yi wa shafin na Facebook. Daga mun fara amfani da shafin muna ‘chatting’ shikenan bamu damu da kulawa ba.

Abubuwan da ya kamata mu kiyaye sun hada da boye sirrukan mu masu muhimmanci irin su lambar waya, Email, shekarun haihuwa (Date of Birth) da sauransu, kuma muke yawan kara saka masa tsaro musamman akwai abubuwan da ake kira code generator, two factors authentication da sauransu.

Ya kamata kuma kasan ‘where you’re logged in’ ko da za ka sayar da wayar ka to ka tabbatar ka sauke shafinka na Facebook daga cikin wayar. Wato za ka yi ‘log out’ kenan. Sannan yana da kyau idan za ka canza waya ka goge dukkan abin da ke kan wayar ta hanyar shiga setting na kan wayar, sai ka shiga ‘factory data reset’.

Mutane da dama suna yawan kuka da yadda ake kwace musu shafinsu na Facebook, alhali shafin yana da muhimmanci a wurin su, wasu na da abokai makusanta da wadanda ke nesa, kamar kasashen waje, kuma ta wannan sahar Facebook din ce kadai suke haduwa, wasu kuwa sun shahara da shafinsu na Facebook din, ma’ana suna da mabiya da yawa wanda lalacewar shafin kan iya haifar musu da matsala ta rashin dawo da wasu cikin mabiyan nasu, ko wani al’amari na siyasa ko kasuwanci da suke tallata wa ta shafin nasu na Facebook.

Sau da yawan lokuta mutane sukan bude shafin Facebook  haka kawai ba tare da bin matakai na Facebook din ba, daga sun bude shafin Facebook din, sukan fara amfani da shi ne kai tsaye ba tare da tunanin seta wasu abubuwa da zai saukaka musu amfani da Facebook din ba, ko kuma kakaba wa shafin tsaro mai yawa domin kiyaye lafiyar shafin Facebook din daga baragurbin mafarauta (Hackers) ba.

Daga lokacin da mutum ya bar shafinsa na Facebook haka kawai ba tare da tsaro ba, ta hanya mai sauki za’a iya kutsawa a bata masa shafin nasa, ko a maka kwacen shafin Facebook gabadaya, sai dai ka ga ana saka abubuwa a shafin naka kai kuma baka sani ba, ko kuma ka ga an tura rokon kudi a wajen jama’a har da wadanda kake jin kunya da ganin girmansu.

Lokacin da aka kwace wa mutum shafinsa na Facebook, abu na farko da suke yi shi ne canza wa mutum makullin sirri ‘password’ sannan su shiga su canza duk wata hanya ko kafar da za a iya bi don dawo da shafin, bayan nan sai su goge duk wani rubutu ko hoto da ke cikin shafin Facebook din (amma idan sun ga dama, domin ba kowane a cikinsu ke yin hakan ba), canza wa mutum hoton dake akan ‘Profile’ dinsa shi ne abu na karshe da suke bayan sun canza wa mutum suna.

Wannan kuwa yakan ba da wahala sosai wajen dawo da shafin Facebook din. Ko da an yi nasarar kwato shafin naka,  to wasu abubuwan ma basa dawowa, sai dai daga karshe ka ji mutum yana cewa ba ya  jin dadin shafin nasa na Facebook din.

Facebook
Ibrahim Sabo
+ postsBio
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Sabuwar Hanyar Kwacen Shafin Facebook (II)
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Sabuwar Hanyar Kwacen Shafin Facebook (I)
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Mene Ne Tsarin 5G?
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Yadda Ake Sarrafa Rubutu Ta Word-Processing

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
Xi Ya Yi Jawabi Ga Taron COP14 Kan Kiyaye Filaye Masu Dausayi

Xi Ya Yi Jawabi Ga Taron COP14 Kan Kiyaye Filaye Masu Dausayi

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.