A yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke halartar taron koli na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO ta shekarar 2026 gami da gudanar da ziyarar aiki a kasar Kyrgyzstan, a yau Lahadi 30 ga watan nan, an yi bikin fara nuna wani shirin bidiyo da kafar yada labarai ta CMG ta kasar Sin ta tsara mai taken “Tsoffin bayanai da Xi Jinping yake so” a Bishkek, fadar mulkin kasar Kyrgyzstan.
Shugaban kasar Kyrgyzstan, Sadyr Japarov, ya aike da sakon taya murnar kaddamar da shirin bidiyon, gami da nuna babban yabo ga wannan aikin hadin gwiwa da aka yi tsakanin kamfanin talabijin da rediyo na Kyrgyzstan da CMG. Kana sakataren shugaban Kyrgyzstan kan harkokin watsa labarai, Askat Alagozov, ya halarci bikin tare da karanta sakon na shugaba Japarov.
A lokacin da aka tsara shirin bidiyon na “Tsoffin bayanai da Xi Jinping yake so”, an fi dora muhimmanci kan fannonin raya tattalin arziki, da kirkiro sabbin fasahohi, da kare muhallin halittu, da tabbatar da ingancin rayuwar jama’a, da dai makamantansu, inda aka dauki dimbin tsoffin bayanai daga littattafai da tarihi na kasar Sin, da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya taba ambata cikin jawaban da ya yi, da rubutattun bayanansa, a kokarin nuna wa masu kallo na kasashe mambobin kungiyar SCO alakar dake tsakanin tunanin shugaba Xi Jinping ta fuskar gudanar da mulki da al’adu da tarihi na kasar Sin, da dabaru da fasahohin kasar wajen daidaita matsalolin da ke damun al’ummun duniya. (Murtala Zhang)














