Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sake yin Allah-wadai da hare-haren ƙyamar baƙi da ƙyamar ƴan Afrika da ake kai wa ’yan Nijeriya da sauran ƴan Afirka a Afirka ta Kudu, yana mai neman shugabannin nahiyar su ɗauki matakin gaggawa domin kawo ƙarshen tashin hankalin da kare mutunci da tsaron ’yan Afrika.
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ne ya isar da sakon shugaba Tinubu a ranar Lahadi yayin taron musamman na 21 na Majalisar Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatocin Tarayyar Afirka (AU) da aka gudanar a Luanda, Angola. Tinubu ya kuma bukaci AU ta sanya batun hare-haren kyamar ƴan Afirka cikin ajandar taronta na yau da kullum da za a gudanar a watan Janairun 2027.
Tinubu ya amince da ƴancin Afirka ta Kudu na tsara dokokin shige da fice da tabbatar da bin dokokinta, amma ya ce hakan bai kamata ya zama dalilin kai wa ƴan Afirka hari ko cin zarafinsu ba. Ya ce irin waɗannan hare-hare na raunana haɗin kan Afirka, da zumunci da zaman lafiya tsakanin ƙasashen nahiyar.
Shugaban ya ce Nijeriya na ganin cewa tattaunawa, da diflomasiyyar rigakafin rikici da haɗin gwiwar ƙasashen Afirka su ne hanyoyin da suka fi dacewa wajen magance matsalar. Ya kuma buƙaci AU ta sake jaddada alhakin kare tsaro da mutuncin ƴan Afirka a duk inda suke zaune a nahiyar.
Kiran shugaba Tinubu ya zo ne yayin da ake ci gaba da samun ƙorafe-ƙorafe kan hare-haren ƙyamar baƙin da ake alaƙanta su da wasu ƙungiyoyin da ke zargin baƙin haure ‘yan Afirka da haddasa rashin aikin yi, ko aikata laifuka da matsin lamba kan ayyukan gwamnati a Afirka ta Kudu.














