ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Likitocin Ƙwaƙwalwa 250 Ne Kacal A Nijeriya, Ragowar Sun Gudu Ƙasashen Waje

by Abubakar Sulaiman
2 weeks ago
Nijeriya

A daidai lokacin da ake bikin Ranar Kula da Lafiyar Ƙwaƙwalwa ta Duniya (World Mental Health Day) a ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba, 2026, sabon rahoton bincike ya bayyana mawuyacin halin da fannin kiwon lafiya ke ciki a Nijeriya, inda ƙwararrun likitocin ƙwaƙwalwa (psychiatrists) 250 kacal ne ke kula da al’ummar ƙasar da ta haura miliyan 200.

Wannan adadi na nuna cewa likitan dake kula da lafiyar ƙwaƙwalwa guda ɗaya kacal ne yake duba kusan kowane mutane 800,000 zuwa miliyan ɗaya, wanda hakan ya yi ƙasa sosai da ƙa’idar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da ta ba da shawarar aƙalla likita ɗaya ga kowane mutum 10,000.

Binciken ya nuna cewa babban abin da ya ƙara taɓarɓare matsalar shi ne yadda ƙwararrun likitoci da ma’aikatan jinya ke ci gaba da ficewa daga Nijeriya zuwa ƙasashen ƙetare (wato matsalar ‘Japa’), musamman zuwa ƙasashen Birtaniya, da Amurka, da Kanada, domin neman ingantaccen yanayin aiki da albashi mai tsoka.

ADVERTISEMENT

Wannan ɓarkewar ƙaura ta bar manyan Asibitocin Kula da Lafiyar Ƙwaƙwalwa na Tarayya (Federal Neuropsychiatric Hospitals) da asibitocin koyarwa na jami’o’i cikin matsanancin ƙarancin ma’aikata.

Ƙungiyar Likitocin Ƙwaƙwalwa ta Nijeriya (Association of Psychiatrists in Nigeria – APN) ta bayyana cewa ƙalubalen matsin tattalin arziƙi, da tsadar rayuwa, da rashin aikin yi, da matsalar tsaro, da hauhawar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi sun haifar da ƙaruwar matsananciyar damuwa (depression), da cututtukan fargaba (anxiety disorders), da kuma yawaitar yunƙurin kashe kai a tsakanin mutane, musamman matasa.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Umarci Hukumomi Su Ƙarfafa Wayar Da Kai Kan Cutar Ebola

Ma’aikatan Lafiya Sun Janye Yajin Aikin Gargaɗi A Katsina

A kan haka, ƙungiyar da sauran masu ruwa da tsaki a fannin lafiya sun buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta hanzarta aiwatar da cikakkun tanade-tanaden Dokar Lafiyar Ƙwaƙwalwa ta Ƙasa (National Mental Health Act), tare da ware kaso na musamman a cikin kasafin kuɗin lafiya domin inganta albashi da walwalar likitoci, da kuma shigar da aikin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa a cikin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHCs) a dukkan ƙananan hukumomin ƙasar.

Nijeriya
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
  • Abubakar Sulaiman
    Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC
  • Abubakar Sulaiman
    Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Umarci Hukumomi Su Ƙarfafa Wayar Da Kai Kan Cutar Ebola
Kiwon Lafiya

Gwamnatin Tarayya Ta Umarci Hukumomi Su Ƙarfafa Wayar Da Kai Kan Cutar Ebola

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Janye Yajin Aikin Gargaɗi  A Katsina
Kiwon Lafiya

Ma’aikatan Lafiya Sun Janye Yajin Aikin Gargaɗi A Katsina

October 19, 2026
Tiyatar Mafitsara Kyauta Ga Mutane 52, Gwamna Yusuf Ya Yaba Wa Saudiyya
Kiwon Lafiya

Tiyatar Mafitsara Kyauta Ga Mutane 52, Gwamna Yusuf Ya Yaba Wa Saudiyya

October 3, 2026
Next Post
Gwamnatin Bauchi Ta Fara Biyan Garatutin Shekarun 2012 Da 2013

Gwamnatin Bauchi Ta Fara Biyan Garatutin Shekarun 2012 Da 2013

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

October 24, 2026
EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

October 24, 2026
Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

October 24, 2026
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.