Jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun shugabancin ƙananan hukumomi 17 a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a faɗin Jihar Yobe.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Yobe (YOSIEC) ce ta sanar da hakan bayan kammala tattara sakamakon zaɓen, inda ta tabbatar da cewa ƴan takarar jam’iyyar mai mulki ne suka yi nasara a dukkan ƙananan hukumomin jihar 17.
Hukumar ta bayyana cewa an gudanar da zaɓen ne a ranar Asabar a faɗin mazaɓu da ƙananan hukumomin jihar cikin kwanciyar hankali da bin doka, tare da samun fitowar masu kaɗa ƙuri’a a rumfuna daban-daban.
A cewar babban jami’in hukumar zaɓen, an ayyana ƴan takarar na jam’iyyar APC a matsayin waɗanda suka lashe zaɓen ne bayan sun cika dukkan ƙa’idojin da doka ta tanada tare da samun mafi yawan ƙuri’un da aka kaɗa, wanda ya haɗa da kwashe kujerun kansiloli a mazaɓun jihar.
Wannan nasara ta sake tabbatar da cikakken ikon jam’iyyar APC a kan harkokin siyasar ƙananan hukumomin Jihar Yobe, yayin da ake sa ran gudanar da bikin rantsar da sababbin shugabannin domin fara gudanar da ayyukansu a hukumance.













