Jiya Laraba, an kaddamar da taron kolin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na shekarar 2026 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin firaministan kasa, Ding Xuexiang, ya halarci taron tare da gabatar da muhimmin jawabi.
Ding Xuexiang ya ce, kasar Sin na ci gaba da inganta cinikayyar hidimomi, inda aka kara bude kofa a wannan bangare, tare da ci gaba da fadada cinikayyar hidimomi, da kuma kyautata tsarin gudanarwar harkokin da abin ya shafa, lamarin da ya samar da karin sabbin damarmmaki ga kasashe da kamfanoni a sassan duniya.
Haka zalika ya ce, a halin yanzu, yanayin tattalin arziki da cinikayya na duniya yana sauyawa cikin sauri, hakan ya sa, habaka cinikayyar hidimomi da kuma karfafa hadin gwiwa a wannan fanni, ba wai kawai zabi na kasar Sin ba ne, har ma na dukkanin kasashen duniya.
Sa’an nan kuma, ya gabatar da shawarwari guda uku: na farko, raya cinikayyar hidimomi zuwa wani sabon mataki ta hanyar habaka sana’o’in ba da hidima cikin inganci. Na biyu shi ne, fadada sabbin fannonin raya cinikayyar hidimomi ta hanyar yin hadin gwiwa da nuna fahimtar juna. Na uku kuma, samar da sabbin karfin raya cinikayyar hidimomi ta hanyar amfani da sabbin fasahohi, kamar fasahar digital da fasahar AI da dai sauransu.
A wannan rana da yamma kuma, Ding Xuexiang ya gana da mataimakin firaministan kasar Bulgaria Alexander Poulev da mataimakin shugaban kasar Zimbabwe Constantino Chiwenga. (Mai Fassara: Maryam Yang)













