Duk da matakan kariya da aka tanada a ɓangaren kiwon lafiyar jama’a da kuma ingantaccen Alluraran da aka samar, kan batun daƙile barazanar yaɗuwar cutar mashaƙu wato a turancen diphtheria, lamarin na ci gaba da faskara.
Yaƙi da wannan cutar, abu ne da ake da mutuƙar buƙatar haɗa ƙarfi da ƙarfe a tsakanin matakan gwamnati uku na ƙasar, domin a daƙile ci gaba da ɓarkewar annobar.
A gefe ɗaya, Cibiyar daƙile yaɗuwar cututtuka ta ƙasa NCDC, ta ruwaito tabbatar da ɓullar ƙwayoyin cutar sama da 10,000, a wasu sassan ƙasar ciki har da jihohin Kano, Katsina, Bauchi da kuma Filato, inda kuma aka samu rasa rayukan da suka kai sama da 300.
Sai dai, Cibiyar ta ce, an samu raguwar rasa rayukan, wanda kuma ta yi gargaɗin cewa, annobar, na ci gaba da zama babbar barazana a fannin kiwon lafiyar ƙasar.Haka zalika, hukumar lafiya ta duniya wato WHO, ta ayyana cutar a matsayin wasu ƙwayoyin cuta, da ke tushe manyan sassan yin numfashi ga waɗanda suka kamu da ita.
Abin da ya sa annobar ke ƙara yin ƙamari shi ne, Allurƙan kaɗai da ake yin amfani da su na yaƙar annobar ba, inda hakan, ke nuna cewa, akwai matuƙar buƙatar, a ƙara ruɓanya yin Alluran ga waɗanda suka kamu da ita, musamman, domin a gina karashi da kuzari tare da kuma inganta garkuwar jikin masu fama da annobar.
Bayan ɓarkewar cutar a 2025 WHO ta ƙiyasta cewa, kimanin ƙananan yara kaso 85 da suka kamu da cutar, wannan kason, ya kai na yawan kimanin ƙananan yara miliyan 110 suka samu shan magungunin ta, sau uku, a rana.Bisa wannan alƙaluman, hakan ya nuna cewa, kaso 15 ko kuma ace, ƙananan yara miliyan 20, ba a iya samar masu da magungunan cutar ba.Amma Cibiyar WHO ta yi nuni da cewa, ƙasahe 83 kacal, ke iya yin Alluranta da ke ɗauke da sanadaran ta, sau uku a rana 42 ke da Alluran da ke ɗauke da ɗaukin sanadaran.
Biyo bayan ɓarkewar cutar a kwanan bayam hakan ya nuna cewa, akwai buƙatar, a ƙara ƙaimi wajen yin rigakafinta ba, ba wai kawai ga yara ba, har da kowa.
Matuƙar ba a ɗauki matakan warkar da it ba, musamman a tsakanin yara, ƙwayoyin annobar za ta iya za ta iya ƙazanta zuwa kaso 30, wanda hakan zai iya haifar da mutuwar yara.Wani bincike da aka wallafa a mujallar kimiyya ta Science Direct ya nuna cewa, ƙasashe marasa ƙarfin arziki, kamar irinsu Nijeriya, ƙaruwar ɓarkewar wannan cutar, na da nasaba da ƙarancin Alluran rigakafinta, rashin kiyaye shirye-shiyen rigakafi da sauransu.
Kusan sama da kaso 60, na ɓullar ƙwayoyin cutar a ƙasar, an ruwaito, sun fi akuwa ne a tsakakin waɗanda, ba a yiwa rigakafinta ba.
A na sa ɓangaren, Darakta Janar na ƙasa na Cibiyar NCDC, Dakta Jide Idris ya danganta rashin gudanar da yin Allurar rigakafin cutar, a matsayin babban abinda ke haifar da ƙara yaɗuwar cutar, wanda ya ce, hakan ya kuma janyo gaza yiwa ƙananan yara da dama, Allurar rigakafin ta.Bugu da ƙari, ya kuma danganta hakan, kan matsalar rashin tsaro, musamman a wasu yankunan ƙasar da ayyukan ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga, ya tarwatsa su, daga muhallansu, inda hakan, ya sanya aka gaza isa ga ƙananan yara da ya kamata, a yiwa Allurar rigakafin cutar.
Haka zalika, ya ce, nauyi ya yiwa kayan kula da kiwon lafiyar da ke a asibitocin ƙasar da kuma rashin samar da wadatattun kayan aikin yaƙar annobar.Sauran manyan matsalolin sun haɗa da, rashin tsafta, rashin samun kulawa da kiwon lafiya, rashin gudanar da bincike a ɓangaren kula da kiwon lafiya da kuma, musamman domin a ɗauki matakan gaggawa da suka kamata. A ra’ayin wannan Jaridar ya zama wajibi a mayar da hankali wajen magance cutar baki ɗaya, ba wai kawai, daƙile ɓarkewar ta ba.
A nan za mu iya cewa, babban abinda ya ya kamata a sanya a gaba shi ne, batun ciki giɓin yin rigafinta da kuma tabbatar da cewa, ba a bar yaro ɗaya a baya, wajen tabbatar da, ya samu maganin rigafinta.
Ya zama wajibi a rinƙa yin rigakafi akai-akai musamman ta hanyar ƙara ƙarfafa tsarin ayyukan asibitocin kula da kiwon lafiya na matakin farko.
Kazalika, akwai matuƙar buƙatar gwamnati, ta gano yankunan da ba a iya shiga domin Allurar rigakafin ba, domin a tabbatar da yiwa yaran rigakafin kaucewa kamuwa da cutar.
Akwai kuma buƙatar a haɗa ƙarfi da ƙarfe a tsakanin matakan gwamnati uku, tare da hukomomin kiwon lafiya, sarakunan gargajiya, malaman addini, ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma abokan haɗaka, domin a lalubo da mafita, kan annobar.Bugu da ƙari, ya wajaba a ƙara ƙarfafa sanya ido, ingnata ɗakunan yin gwaje-gwaje, bai wa malaman kiwon lafiya goyon bayan da ya dace, musamman domin yin gwaje-gwajen cutar da kuma ɗaukar matakan kare yaɗuwar annobar.
Muna goyon bayan kiran da Cibiyar NCDC ta yi, na kira ga matakan gwamnati ukun, kan gano yankunan da ba a iya kutsawa, domin yin rigakafin cutar ba, musamman domin a cikin giɓin da ake da shi, na yaƙar annobar.A ɓangaren ‘yan Nijeriya kuwa, ya zamar masu wajibi, su koyi ɗabi’ar shan tsaftataccen ruwan sha, gyra muhallansu, da kuma tabbatar da, suna yawan wanke hanayensu, da Sabulu, domin yin rigakafin cutar.
Kazalika, ya zama wajibi, sun gujewa ɗabi’ar yin bahaya barkatai, musamman a hanyoyin da ruwa ke wucewa, domin a daƙile yaɗuwarta.Hatta abinci, kariyar da ta kamata, musamman, domin a kaucewa cin gurɓataccensa.
Cutar dai, na ci gaba da laƙume rayuwar ‘yan Nijeriya, musamman ƙananan yara, inda wannan ɓarkewar za ta zama, tamkar kira ga matakan gwamnati ukun da sauran yankuna, domin bai wa yaran kariyar da kamata.













