Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya fito ya yi wa al’ummar Nijeriya cikakken bayani game da ci gaba da hauhawar basussukan da ake bin ƙasar.
Atiku ya nuna damuwarsa kan yadda adadin bashin Nijeriya ke ci gaba da ƙaruwa cikin sauri, inda ya bayyana cewa hakan na zama babbar barazana ga makomar tattalin arziƙin ƙasar. Ya ce: “Wajibi ne gwamnati ta fito fili ta yi wa ƴan ƙasa bayani kan dalilan da suka sa ake ci gaba da karɓar sababbin basussuka duk da matakan tara kuɗin shiga da aka ɗauka.”
A cewar tsohon mataimakin shugaban ƙasar, duk da ƙarin kuɗaɗen shiga da gwamnatin tarayya ke samu bayan aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziƙi, har yanzu ba a ga wani gagarumin aikin ci gaba da zai kare ƙasar daga faɗawa cikin mawuyacin halin bashi ba.
Haka kuma, Atiku ya jaddada cewa ƴan Nijeriya suna da cikakken haƙƙin sanin yadda ake kashe kuɗaɗen da ake karɓowa a matsayin bashi da kuma dabarun da gwamnati ke da su na biyan waɗannan basussuka a nan gaba ba tare da ya shafi jin daɗin al’umma ba.
A ƙarshe, ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da cin basussuka marasa tsari, yana mai kiran mahukunta da su mayar da hankali wajen rage ɓarnatar da kuɗaɗen gudanar da mulki da kuma bunƙasa hanyoyin samun kuɗi na cikin gida domin ciyar da Nijeriya gaba.














