Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu
A yau Lahadi, shugaban kasar Sin, Xi Jinping da Sarki Philippe na Belgium, sun taya juna murna bisa cika shekaru 55 da kulla alakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu. Xi ya nuna cewa, a cikin shekaru 55 da suka gabata tun bayan kulla alakar diflomasiyyar, Sin da Belgium sun yi riko da ka'idojin girmama juna, daidaito, cin gajiyar juna da hadin gwiwa mai amfanar da juna, kuma dangantakar kasashen biyu ta bunkasa ba tare da tangarda ba. Xi ya bayyana cewa yana ba da muhimmanci sosai ga ci gaban alakar da ke tsakanin kasar Sin da Belgium, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da Sarki Philippe domin ba da jagoranci ga huldar abota da hadin gwiwa mai zurfi tsakanin kasashen biyu zuwa sabbin matakai na koli, tare da bayar da sabbin gudummawa wajen karfafa kyakkyawar alaka tsakanin Sin da Tarayyar Turai (EU) ba tare da tangarda ba. A cikin sakonsa kuwa, Sarki Philippe ya ce ya yi amannar cewa bangarorin biyu za su gina a kan nasarorin da aka samu cikin shekaru 55 da suka gabata, domin kara inganta tattaunawa mai bude kofa, fadada hadin gwiwa a aikace, da kuma zurfafa fahimtar juna. Ya ce, kasar Belgium a shirye take ta bunkasa dangantaka bisa daidaito da amfanar da juna tare da kasar Sin, da tunkarar dimbin kalubalen duniya na bai-daya, da karfafa zaman lafiya, kwanciyar hankali, da kuma ci gaba mai dorewa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)



















