Dawowar Taiwan Babban Yankin Sin: Kasashe Masu Tasowa Ba Za Su Bari Hannun Agogo Ya Koma Baya Ba
Daga ranar 23 zuwa 25 ga wata, kasashen Afrika 5 sun karbi bakuncin bikin nune-nunen hotuna, albarkacin cikar yankin Taiwan shekaru 81 da dawowa karkashin ikon mulkin kasar Sin. Kasashen 5 na Afrika sun hada da Kenya da Nijeriya da Afrika ta Kudu da Tanzania da kuma Mozambique. A shekarar 2025, kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ya yanke shawarar ayyana ranar 25 ga watan Oktoba a matsayin ta tunawa da Dawowar Taiwan Babban Yankin Sin, da kokarin kare nasarorin yakin duniya na II da ma odar duniya bayan yakin. Me karbar bakuncin wadannan nune-nune da kasashen Afrika suka yi yake nufi? Amincewa da kiyaye manufar “kasar Sin daya tak a duniya,” da kasancewar Taiwan wani bangare na kasar da ba zai iya ballewa ba, ita ce tushen kulla dangantaka tsakanin Sin da daukacin kasashen duniya. Batun da ya shafi yankin Taiwan, batu ne mai muhimmanci ga kasar Sin, kuma batu ne na cikin gida. Don haka, ba shakka yadda kasashen Afrika suka karbi bakuncin nune-nune ya kara tabbatar da yadda suke girmama cikakken ’yancin Sin da iko kan yankunanta. Ya kara bayyana mana kyakkyawar alakar dake tsakanin bangarorin biyu, domin ya nuna cewa, yadda Sin ke tsaya musu a dandalin kasa da kasa da yadda take goyon bayan ci gabansu, su ma suna girmama burika da muradunta. Wannan ita ce abota ta kwarai da aminci bisa mutuntawa da girmama juna. Duk da cewa wasu kasashe na ingizawa tare da aikewa da mummunan sako ga masu neman ballewa da samun ’yancin kan Taiwan, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kare nasarorin da aka samu bayan yakin duniya na II. Cikin shekaru 81 da suka gabata, daya daga cikin nasarori mafiya muhimmanci ita ce, kokarin Sin na ci gaba da tabbatar da kasancewar Taiwan wani bangare na kasar, da kokarin tabbatar da dunkulewar kasar da ma son ganin ci gaban yankin, kamar yadda ya dace babbar kasa ta yi. Wannan kadai, ya isa nunawa masu neman ballewa da magoya bayansu cewa, hakarsu ba za ta taba cimma ruwa ba. Kuma yayin da tsarin duniya ya sauya, watau kai ya waye, kasashe masu tasowa suke samun ci gaba cikin sauri da kokarin dogaro da kansu (godiya ga kasar Sin), ba za su bari hannun agogo ya koma baya ba, za su hada hannu da Sin wajen samar da duniya mai daidaito da adalci da rarrabuwar iko tsakanin kasa da kasa. Kuma ba makawa za su bayar da gagarumar gudunmuwa wajen ganin dunkulewar dukkanin yankunan Sin wuri guda, maimakon ballewar wani yanki. (Fa’iza Mustapha)



















