An Cimma Yarjejeniyoyi Da Dama A Zagaye Na 8 Na Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayyar Sin Da Amurka
A yayin taron manema labarai na yau da kullum da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta gudanar da yinin yau, mai magana da yawun ma'aikatar, He Yadong, ya yi bayani kan batun da ya shafi zagaye na takwas na tattaunawar tattalin arziki da cinikayya, wadda tawagogin Sin da Amurka suka gudanar a birnin New York na kasar ta Amurka. He Yadong ya gabatar da cewa, a kwanan nan, tawagogin tattalin arziki da kasuwanci na kasashen biyu sun gudanar da zagaye na takwas na tattaunawar tattalin arziki da cinikayya a Amurka. Bangarorin biyu sun yi shawarwari masu zurfi na gaskiya da gaskiya, kan batutuwan tattalin arziki da cinikayya da suka shafe su, kamar aiwatar da yarjejeniyar matsayar da aka cimma a tattaunawar tattalin arziki da cinikayya, da aiwatar da tsare-tsaren rage haraji daidai-wa-daida, da kuma kafa majalisun cinikayya da zuba jari, kana sun cimma wasu matsaya da dama. Kazalika, bangarorin biyu sun kuma tattauna a karon farko game da fasahar kirkirarriyar basira ta AI a karkashin tsarin tattaunawar tattalin arziki da cinikayyar Sin da Amurka. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)



















