Tsohon kyaftin ɗin tawagar Super Eagles ta Nijeriya, William Troost-Ekong, ya karɓi addinin Musulunci bayan ya karanta kalmar shahada a birnin Doha na ƙasar Qatar.
Rahotanni sun ce Ekong ya bayyana musuluntarsa ne a wani zama da ya yi da wasu malaman addinin Musulunci a Doha.
Jaridar Qatar Al-Arab ce ta fara wallafa labarin a ranar Laraba, inda ta ce ɗan wasan ya karanta kalmar shahada a wajen taron.
Wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta ya nuna Ekong yana karanta kalmar shahada.
Shahararren malamin Musulunci, Dr Muhammad Salah, shi ma ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana Ekong a matsayin Musulmi.
Rahoton ya kuma samu karɓuwa daga wasu kafafen yaɗa labarai na duniya, ciki har da jaridar wasanni ta Morocco, Elbotola, da jaridar Masar, Youm7.
Ekong, mai shekaru 33, yana taka leda a ƙungiyar Al-Ahli Doha ta Qatar Stars League.
Ya koma ƙungiyar a shekarar 2026 kan kwantiragin shekara ɗaya da rabi bayan ya bar Al-Kholood ta Saudiyya.
Ya wakilci Nijeriya a wasanni sama da 70, ciki har da gasar Kofin Duniya ta 2018 da aka gudanar a Rasha.
Ekong ya kuma taka muhimmiyar rawa a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2023 da aka gudanar a Ivory Coast, inda Nijeriya ta kai wasan ƙarshe.
A wannan gasar, an ba shi kyautar Gwarzon Ɗan Wasa na Gasar, bayan ya taimaka wa Super Eagles wajen kaiwa wasan ƙarshe tare da zura ƙwallaye uku a raga a gasar.














