ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

El-Rufai Ya Magantu Kan Abokansa Da Suka Yi Shiru Yayin Da Yake Tsare A Hannun ICPC

by Sadiq
43 minutes ago

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi magana kan yadda wasu daga cikin tsofaffin abokan aikinsa, abokansa da mutanen da suka taɓa taimako suka yi shiru a lokacin da ake tsare da shi.

A cikin wata sanarwa mai taken “My Relationships and the Aftermath”, wadda ya wallafa a shafinsa na Facebook, El-Rufai ya ce ya taimaki mutane da dama a kan abin da ya yi amanna a kai.

Ya ce bai taɓa taimaka wa mutane da nufin su saka masa ba idan ya shiga wani hali.

ADVERTISEMENT

El-Rufai ya ce mutanen da ya taɓa taimaka wa suna da damar zaɓar yadda za su mayar da martani game da halin da yake ciki.

Ya ce suna iya mara masa baya, ko su yi shiru ko kuma nesanta kansu daga gare shi.

LABARAI MASU NASABA

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Bai Wa ’Yan Bindiga Bayanai A Sakkwato

‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sa-kai 3, Rami Ya Rufta Kan Masu Haƙar Ma’adinai 4 A Filato

Ya ƙara da cewa ba ya son yanke hukunci kan abin da wasu suka yi a gare shi.

Tsohon gwamnan ya ce lokacin da mutane ke fuskantar ƙalubale a rayuwa, yana koyon darasi daga abubuwan da suke faruwa ya fahimci yadda alaƙarsa ta ke da jama’a.

Sai dai ya jaddada cewa bai kamata a yi amfani da lamarinsa wajen zargin kowa ba.

El-Rufai ya kuma ce ba ya nadamar taimaka wa mutane a lokacin da ya yi imanin cewa yin hakan shi ne abin da ya dace.

Game da zargin rashin adalci da sauran abubuwan da ake dangantawa da halin da yake ciki, El-Rufai ya ce ba zai ɗauki fansa ba, yana mai cewa zai bar hukuncin komai a hannun Allah.

El-Rufai yana tsare a hannun ICPC tun a watan Fabrairun 2026, sakamakon zarge-zargen almundahanar kuɗaɗe da amfani da ofishinsa ba bisa ƙa’ida ba, sai dai ya musanta dukkan zarge-zarge.

Ya shigar ƙara a Babbar Kotun Tarayya, inda ya nemi Naira biliyan ɗaya a matsayin diyya kan tsare shi ba bisa ƙa’ida ba.

Ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da yi masa bita da ƙulli irin na siyasa, zargin da gwamnati da hukumomin da abin ya shafa suka ƙaryata.

MASU ALAKA

Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato
Manyan Labarai

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Bai Wa ’Yan Bindiga Bayanai A Sakkwato

September 24, 2026
’Yan Bindiga Sun Sace Matafiya 28 A Jihar Filato
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sa-kai 3, Rami Ya Rufta Kan Masu Haƙar Ma’adinai 4 A Filato

September 24, 2026
Sultan
Manyan Labarai

Sultan Ya Gargaɗi Malaman Addini Kan Kare Masu Cin Hanci Da Rashawa

September 23, 2026
Next Post
Sin Ta Yi Kira Da A Karfafa Ci Gaban Fasahar AI Ta Yadda Za Ta Amfani Jama’a Da Kyautata Rayuwarsu

Sin Ta Yi Kira Da A Karfafa Ci Gaban Fasahar AI Ta Yadda Za Ta Amfani Jama’a Da Kyautata Rayuwarsu

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Da A Karfafa Ci Gaban Fasahar AI Ta Yadda Za Ta Amfani Jama’a Da Kyautata Rayuwarsu

Sin Ta Yi Kira Da A Karfafa Ci Gaban Fasahar AI Ta Yadda Za Ta Amfani Jama’a Da Kyautata Rayuwarsu

September 24, 2026
Kotu Ta Umarci A Kamo Mata Dogarin Gwamna El-Rufa’i

El-Rufai Ya Magantu Kan Abokansa Da Suka Yi Shiru Yayin Da Yake Tsare A Hannun ICPC

September 24, 2026
An Cimma Yarjejeniyoyi Da Dama A Zagaye Na 8 Na Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayyar Sin Da Amurka

An Cimma Yarjejeniyoyi Da Dama A Zagaye Na 8 Na Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayyar Sin Da Amurka

September 24, 2026
Sin Na Aiwatar Da Kwararan Matakan Ingiza Ci Gaban Duniya

Sin Na Aiwatar Da Kwararan Matakan Ingiza Ci Gaban Duniya

September 24, 2026
Firaministan Sin: Karfafa Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Da Masu Ci Gaba A Fannin Cinikayyar Fasahohin Zamani

Firaministan Sin: Karfafa Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Da Masu Ci Gaba A Fannin Cinikayyar Fasahohin Zamani

September 24, 2026
Xi Jinping Ya Isa Washington DC Don Ziyarar Aiki a Amurka

Xi Jinping Ya Isa Washington DC Don Ziyarar Aiki a Amurka

September 24, 2026
Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Bai Wa ’Yan Bindiga Bayanai A Sakkwato

September 24, 2026
Tsohon Kyaftin Super Eagles William Troost-Ekong Ya Karɓi Musulunci A Qatar

Tsohon Kyaftin Super Eagles William Troost-Ekong Ya Karɓi Musulunci A Qatar

September 24, 2026
’Yan Bindiga Sun Sace Matafiya 28 A Jihar Filato

‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sa-kai 3, Rami Ya Rufta Kan Masu Haƙar Ma’adinai 4 A Filato

September 24, 2026
Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

September 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.