An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou
A yayin da ake cika shekaru 81 da maido da Taiwan kasar Sin kuma cika shekara daya da kafa ranar maido da Taiwan kasar Sin, an gudanar da taron karawa juna sani na murnar cika shekaru 81 da maido da Taiwan kasar Sin a birnin Fuzhou dake lardin Fujian na kasar Sin a yau Lahadi 25 ga wannan wata. A gun taron, direktan ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin kuma na majalisar gudanarwar kasar Sin, Song Tao, ya bayyana cewa, jam’iyyar kwaminis ta Sin da kuma gwamnatin kasar Sin sun kafa ranar maido da Taiwan kasar Sin don shaida imanin kasar Sin na tabbatar da ikon mallakar kasa da kiyaye martabar yankunan kasar, da kuma tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya. Ya kamata jama’ar gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan su bi tunanin yaki da hare-hare tare da raya al’ummar kasar, da kin amincewa da duk wani irin yunkurin ‘yan aware na yankin Taiwan da kuma tsoma baki daga waje kan batun. (Zainab Zhang)



















