Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Ta Yi Watsi Da Nuna Fuska Biyu Da Kuma Amfani Da Yaudarar Siyasa
An ruwaito cewa jami'an ma'aikatar shari'a ta Amurka sun bayyana cewa Amurka ta kwace wasu shafukan intanet guda bakwai da ake zargin suna da alaka da wasu Sinawa masu kutsen shafin intanet, wadanda suka yi kokarin keta hurumin tsare-tsaren na’urorin ababen more rayuwa a Amurka da kuma sauran wasu kasashe. A matsayin martani ga wannan, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning, ta bayyana cewa kasar Sin na matukar adawa da ayyukan kutsen shafukan intanet kuma tana fatattakar su bisa tanadin doka. Kazalika, kasar Sin na matukar adawa da yada bayanai marasa tushe balle makama da kuma tayar da hayaniya domin cimma manufofin siyasa. Kasar Sin tana kira ga bangaren Amurka da ya daina nuna fuska biyu da kuma amfani da yaudarar siyasa, kana ya yi aiki tare da kasar Sin ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna bisa tushen daidaito, domin tunkarar barazanar tsaron shafukan intanet cikin hadin gwiwa tare da gina dangantaka mai cike da zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da mutunta juna dangane da batutuwan shafin intanet. A wani labarin kuma, a martanin da ta mayar kan kokarin da masu ra’ayin rikau na kasar Japan ke ci gaba da yi na jirkita tarihin yakin duniya na biyu ta hanyar shigar da gurbatattun bayanai cikin manyan samfuran manhajojin AI, Mao Ning ta bayyana cewa amfani da sabbin fasahohi don lalata hakikanin bayanan ya kasance wata sabuwar hanyar da masu ra’ayin rikau na Japan ke amfani da ita wajen gurbatawa da kuma kambama tarihin yakin Japan. Manufar hakan ita ce a cusa wata bahaguwar fahimta a tarihin yakin duniya na biyu, da kawar da adawar jama'a da sake afkawa yaki bayan samun zaman lafiya da kuma hanzarta sake tara karfin soji a Japan. (Abdulrazaq Yahuza Jere)



















