A jiya Talata 6 ga watan nan, wato ranar kusa da ta karshe a kwanaki bakwai na hutun bikin murnar zagayowar ranar kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar, adadin kudaden da gidajen sinima na kasar Sin suka tara ya kai sama da yuan biliyan daya, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 149.2, lamarin da ake dangantakawa da muhimmiyar rawar da fina-finan cikin gida na Sin suka taka a wannan fage. (Saminu Alhassan)
ADVERTISEMENT














