Ko Zai Yiwu a Samu Mai Cuta Daban, Mai Shan Magani Daban?
Shin zai yiwu wani mutum bayan ya kamu da cuta, sai ya sa sauran mutane shan magani a madadinsa? Ta wannan hanya zai iya samun waraka kuwa? Sanin kowa ne, hakan ba zai yiwu ba. Duk da haka, abun da ya yi kama da wannan misali ya kan faru a duniyarmu. A kwanan nan, wasu kasashe sun ce wai an kaskantar da darajar musanyar kudin kasar Sin wato RMB da gangan, har ma sun ce za su tilasta kasar Sin don ta daga darajar kudin. Nufinsu shi ne, da farko, suna tsammanin cewa kasar Sin ta rage darajar kudinta don neman samun fifiko wajen fitar da kayayyakinta zuwa ketare. Kuma na biyu shi ne, idan an sa darajar kudin Sin ta karu, to, za su samu damar daidaita matsalar da suke fuskanta ta karancin fitar da kayayyaki zuwa ketare. Dangane da zancensu, babban bankin kasar Sin, wato bankin jama'ar kasar Sin ya gabatar da wata takarda a jiya Alhamis, wadda ta bayyana ra'ayin gwamnatin kasar dangane da darajar musanyar kudin RMB. A cikin takardar, an ce, da farko, kasar Sin na aiwatar da manufar musanyar kudi bisa tushen la'akari da bukatun kasuwa, kana ta daina daukar matakin kayyade darajar kudinta na yau da kullum tun daga shekarar 2017, wato ba ta juya akalar darajar musanyar kudin RMB. Sa'an nan na biyu shi ne, babu wata alakar kai tsaye tsakanin darajar musanyar kudi da yanayin ciniki, ma'ana, ko da yake kasar Sin ta fi fitar da kayayyaki bisa kwatantawa da darajar kayayyakin da ta shigar da su daga ketare, amma hakan ba ya nufin cewa ya kamata a daga darajar musanyar kudin RMB. Sa'an nan na 3 shi ne, kasar Sin ba ta bukatar neman samun fifiko a fannin ciniki ta hanyar rage darajar kudinta, kuma ba ta da niyyar yin haka. A akasin haka, kasar tana kawo sauye-sauyen salonta na raya tattalin arziki, da habaka bukatun cikin gida, da fadada bude kofa ga kasashen waje, a kokarin tabbatar da daidaituwar yanayin tattalin arzikin duniya. Hakika ra'ayin gwamnatin kasar Sin ya yi daidai da na dimbin masana ilimin tattalin arziki na kasashe daban daban. Misali, tsohuwar babbar masaniyar ilimin tattalin arziki ta asusun lamunin duiya (IMF), Gita Gopinath, da tsohon babban masanin ilimin tattalin arziki na IMF, Pierre-Olivier Gourinchas, da farfesa ta jami'ar koyon ilimin kasuwanci ta London dake kasar Birtaniya, Helene Rey, sun yi hadin gwiwa wajen rubuta wata makala don a wallafa ta a mujallar the Economist ta kasar Birtaniya, inda suka bayyana cewa, bai kamata a ce musabbabin matsalar da cinikin duniya ke fuskanta yanzu shi ne raguwar darajar musanyar kudin Sin ba. A cewarsu, darajar musanyar kudin RMB ta kasance a wani matsayi mai karko a shekarun nan, kana raguwar darajar kudin RMB da aka samu a kwanakin nan, ba domin “juya akalar darajar kudi” ne ake samunta ba, a’a, dalilin da ya sa hakan ya faru shi ne domin kasar Sin ba ta fama da hauhawar farashin kayayyaki mai tsanani kamar abokanta na ciniki. Ban da haka, a cewar wadannan masanan ilimin tattalin arziki uku, ko da an daga darajar kudin Sin sosai ma ba zai haifar da manyan sauye-sauye ga yanayin cinikin duniya ba, saboda karuwar darajar kudin Sin zai sa bukatar kasar kan kayayyakin sauran kasashe ta ragu. Sai dai idan mun yi bincike kan ainihin dalilin da ya sa kasashen Turai da kasar Amurka fuskantar mawuyacin hali a fannin fitar da kayayyakinsu, shi ne domin yadda suke dogaro kan bangaren hada-hadar kudi fiye da kima, da lalacewar bangaren masana’antunsu. Matakan da ya kamata su dauka sun hada da daidaita yanayin da suke ciki na karancin ajiyar kudi, da kashe kudi fiye da kima, da yawan cin bashi don biyan bukatar gudanar da ayyukan gwamnati, gami da inganta tsare-tsarensu a fannin masana’antu, maimakon dora wa kasar Sin laifi a-kai-a-kai. (Bello Wang)



















