Sin Ta Mika Tallafin Dala Miliyan 2 Ga Kenya Domin Yaki Da Cutar Ebola Da Rage Radadin Fari
Gwamnatin kasar Kenya ta karbi tallafin kudi daga kasar Sin, jimillar dalar Amurka miliyan 2 domin kara kaimi wajen yaki da cutar Ebola da kuma rage radadin fari da take fuskanta. Jakadiyar kasar Sin a Kenya Guo Haiyan da babban sakataren asusun baitilmali na kasar Kenya Chris Kiptoo da babbar sakatariyar ma’aikatar kula da lafiyar al’umma Mary Muthoni sun halarci bikin mika kudin da ya gudana a jiya Alhamis a ma’aikatar kudi ta Kenya dake Nairobi, babban birnin kasar, inda bangarorin biyu suka sanya hannu. Gwamnatin kasar Sin ta bayar da tsabar kudi dalar Amurka miliyan 1 kamar yadda gwamnatin Kenya ta nema, domin karfafa shirye-shiryen dakile yaduwar cutar Ebola a kasar bayan samun rahoton bullar ta. Ragowar dala miliyan 1 kuma gwamnatin kasar za ta yi amfani da su domin daukar matakan dakile tasirin fari a kasar. Kiptoo ya yabawa kasar Sin bisa yadda ta amsa rokonsu a kan lokaci da kuma bayar da tallafin kudin, domin kara musu kaimi wajen dakile yaduwar cutar Ebola da magance illar fari. A ranar Talata ne Kenya ta sanar da rahoton bullar cutar, bayan wani ‘dan kasar ya dawo gida bayan shafe shekaru bakwai yana zaune a Jamhiriyyar Demokradiyyar Congo, inda ya rasu sakamakon kamuwa da cutar a wani asibiti da ke birnin Nairobi. (Mai fassara: Suleiman Suleiman) )



















