Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun, ya bayyana a yau Laraba cewa, kasar Sin ta damu matuka game da ci gaba da tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, kuma tana adawa da hare-haren da ake kai wa wurare na fararen hula kamar filayen jiragen sama.
Ya kara da cewa, kasar Sin tana kira ga bangarorin da abin ya shafa da su warware takaddamarsu ta hanyar tattaunawa da sulhu, domin taimaka wa dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya cikin hanzari.
Guo ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai na yau da kullum, bayan an nemi ya yi tsokaci game da sabbin hare-haren da kungiyar Houthi ta kasar Yemen ta kai kasar Saudiyya.
Game da abin da aka ruwaito kwanan nan a Singapore na cewa, shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya yi kira da a rage dogaron da ake yi da kasar Sin, ya kuma bayyana cewa manufar Jamus game da kasar Sin tana kara zama babba kuma ta yi daidai da manufar Tarayyar Turai.
Dangane da hakan, Guo ya bayyana fatan cewa Jamus da Tarayyar Turai za su kasance masu adalci da tunani na hankali, tare da yin aiki a kan tafarki guda da kasar Sin, ta yadda za su iya zama abokan hulda masu amincewa da juna kuma wadanda za su iya hasashen matakan juna, da warware sabani da takaddama ta hanyar tattaunawa da shawarwari, da tabbatar da cewa tsarin masana’antu da na samar da kayayyaki na duniya sun kasance cikin kwanciyar hankali ba tare da tangarda ba, da kuma samar da karin tabbaci ga hadin gwiwa tsakanin al’ummominsu na ‘yan kasuwa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)













