Kasashen Sin da Ghana da wasu karin kasashe 24, sun zamo na farko da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar MDD ta inganta tsarin hada-hadar dakon hajoji. An sanya hannu kan yarjejeniyar ne yayin wani biki da ya gudanar a ranar Litinin a birnin Accra na kasar Ghana.
Da yake tsokaci yayin sanya hannun, mataimakin ministan cinikayya na kasar Sin, wanda kuma shi ne ya sanya hannu a madadin kasarsa, mista Jiang Chenghua ya ce kirkire-kirkire tsakanin hukumomi na cike gibin dake akwai a fannin aiwatar da kaidojin kasa da kasa, da kyautata tsarin aiwatar da dokokin kasa da kasa a fannin hada-hadar kudi dake bukatar takardun sufuri tsakanin kan iyakoki.
Jiang, ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkan sassan da suka sanya hannu kan yarjejeniyar, domin kammala amincewa da takardun tabbatar da ita a kan lokaci. Kazalika, jamiin ya ce Sin na fatan karin kasashen duniya za su rungumi yarjejeniyar, ta yadda amfaninta zai isa zuwa karin kasashe, tare da samar da gudunmawa ga ci gaban cinikayyar kasa da kasa da walwalar daukacin alummun duniya baki daya.
A nata bangare kuwa, sakatariyar hukumar lura da dokokin cinikayyar kasa da kasa karkashin MDD ko UNCITRAL Anna Joubin-Bret, cewa ta yi yarjejeniyar za ta taimaka wajen rage rashin tabbas, da ingiza hada-hadar samar da kudaden cinikayya, da tallafawa zamanantar da cinikayya zuwa salon dijital, da kyautata ingancin tsarin hada-hadar masanaantun kasa da kasa. Daga nan sai ya godewa gwamnatin kasar Sin bisa gabatarwa UNCITRAL wannan yarjejeniya
Kimanin wakilai 400 daga sama da kasashe da yankunan duniya 60 ne suka halarci bikin sanya hannu kan yarjejeniyar, wadda kasar Sin ta kirkiro da daukar nauyin gabatarwa, kuma ta samu amincewar zama na 80 na babban taron MDD na watan Disamban shekarar 2025. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














