Fu Cong, wakilin Sin na dindindin a MDD, ya yi jawabi jiya 27 a yayin taro kan batun nukiliyar Iran da kwamitin sulhun MDD ya shirya, inda ya jaddada cewa, ya kamata bangarorin da abin ya shafa wato Amurka da Iran su dakatar da bude wuta, tare da ingiza yin tattaunawa cikin ruwan sanyi.
Fu Cong ya nuna cewa, ficewar Amurka daga cikakkiyar yarjejeniyar batun nukiliyar Iran daga gefenta, da sake dawo da takunkumin da ta kakkaba wa Iran da kuma kara tsananta shi, da daukar matakin “matsin lamba mafi tsanani”, su ne dalilan dake dagula rikicin da ake fuskanta a tsakaninsu yanzu.
Fu Cong ya jaddada cewa, siyasa da diflomasiyya ita ce kadai hanyar warware matsalar nukiliyar Iran. Iran ya kamata ta cika alkawarinta na daina bunkasa makaman nukiliyarta, kuma ya kamata bangarorin da abin ya shafa su mutunta hakkin Iran na amfani da makamashin nukiliya cikin zaman lafiya a matsayinta na mai rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.
Amurka ya kamata ta yi alkawarin ba za ta sake kai wa Iran hari ba, da kuma tabbatar da gudanar da ayyukan sa ido bisa yanayi maras tursasawa da karfin soji.
A wannan ranar kuwa, Fu Cong ya yi jawabi a yayin babban taron MDD kan batun “Dole ne Amurka ta daina yiwa tattalin arziki da kasuwanci da harkar kudi na Cuba kangiya”, inda ya bukaci Amurka da ta daina toshewa da matsin lamba kan Cuba nan take. Kana a cewarsa, ba shakka dole ne a bar makomar Cuba a hannun al’ummar Cuba dogaro da karfin kansu.
Fu Cong ya kuma jaddada cewa, idan babu izinin kwamitin sulhu na MDD, takunkumin da ake kakkabawa ba shi da tushe bisa dokokin kasa da kasa. (Amina Xu)














