A tsakiyar birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan na kasar Sin, akwai wani tsibiri da ake kira da Tsibirin Lemu, wanda ya zarce zama wurin yawon bude ido kawai, bisa yadda ya kunshi tarihi da kafa sabon tunanin falsafar siyasa a tarihin kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin. Tsibirin yana nan a tsakiyar Kogin Xiang, kuma ya shahara saboda alakarsa da shugaba Mao Zedong, babban jagora a cikin jiga-jigan da suka taka muhimmiyar rawar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin.
A ziyarar da muka kai kwanan nan, yanayin wurin ya kasance mai ni’ima, kana akwai bakin yawon bude ido da suka zo tawaga-tawaga daga cikin gida da sassa daban-daban na duniya, domin fahimtar tarihin siyasa da akidun da suka taimaka wajen gina tsarin shugabanci na kasar Sin. Daga cikin tawagogin akwai wasu baki da muka kasance da su cikin tawaga daya daga kasar Laos, wadanda, bisa bayanin da muka samu, sun zo ne domin nazarin akidu da manufofin Jam’iyyar Kwaminis ta Sin (JKS) daga tushe. Wannan ya nuna cewa Tsibirin Lemu, ba wuri ne na yawon shakatawa saboda ni’imarsa ba, ga wasu makaranta ce ta tarihi.
Changsha, babban birnin lardin Hunan wanda tsibirin yake, ya kasance wurin da Mao Zedong ya yi shekarun samartakarsa inda a lokacin ne ya bunkasa tunaninsa na siyasa. A wannan birni ne ya yi karatu, ya yi mu’amala da wasu matasa masu kishin kawo sauyi, tare da fara zurfafa tunani kan makomar al’ummar Sin. Kuma hakan ya sa birnin zamowa daya daga cikin muhimman wuraren da aka samu muhawara, da shirye-shirye, da kungiyoyin matasa wadanda suka taka rawa a tarihin juyin-juya-halin kasar Sin. Saboda haka, birnin ya kasance mai alaka sosai da tarihin kafuwar JKS.
Daga bayanan da na tattaro, an ce a shekarar 1925, Mao ya je Tsibirin Lemu, inda ya rubuta shahararriyar wakarsa ta “Qinyuan Chun: Changsha”, wakar da ta bayyana yanayin kaka, da Kogin Xiang da tunanin matasa game da makomar kasarsu. An kwafi wannan waka ta asalin rubutun Mao tare da wallafa ta a wani dutse da ke tsibirin.
Kazalika, wani abin da ya fi daukar hankali a Tsibirin Lemun shi ne babban mutum-mutumin Mao Zedong da aka yi na dutse mai siffarsa ta lokacin da yake dan shekaru 32 a duniya. An kammala gina shi a tsibirin ne ranar 26 ga Disamban 2009, ranar da aka yi bikin cika shekaru 116 da haihuwar Mao. Mutum-mutumin yana da tsawon mita 83 daga farkon kafadar dama zuwa ta hagu, da kaurin mita 41 da kuma tsayin mita 32 daga kasa. Idan aka tsaya ta gabansa, ana iya lura da yadda kamanninsa ke bayyana ta hanyoyi daban-daban, gwargwadon kusurwar da mutum yake kallo. A wasu kusurwoyi, musamman idan aka kalli fuskar daga gefe, kamanninsa na iya ba da hoton mutum mai zurfin tunani, wanda ya mai da hankali kan abin da ke gabansa.
Gashinsa ma ya ja hankalina bisa yadda aka tsara shi, saboda yadda yake ba da kamannin matashi mai rayuwa a lokacin gwagwarmaya. Wata jami’a mai mana jagoranci a wurin ta ce, wannan siffa tana iya sa mai kallon mutum-mutumin ya fahimci cewa, Mao a lokacin, matashi ne da yake fuskantar neman amsar tambayoyi game da makomar al’ummarsa.
Hakika wadanda suka yi zanen sun nuna kwarewa da fasahar sana’arsu, sauran bayani kuma, abin sai wanda ya gani. Kuma muhimmin abin lura a nan shi ne cewa mutum-mutumin ba dutse ne kawai ba, alama ce ta tunatarwa kan wani zamani na tarihin gwagwarmayar kafa tubalin kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














