Shugaba Bola Tinubu, zai bar Abuja a ranar Alhamis domin zuwa birnin Makka da ke Saudiyya don yi wa Nijeriya addu’a.
A cewar sanarwar da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu zai yi addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai, kwanciyar hankali da ci gaba a Nijeriya.
Kafin ya bar Abuja, shugaban ƙasar zai ƙaddamar da sabbin kayan aikin da Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ta saya, a ɓangaren saukar jiragen shugaban ƙasa na filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
ADVERTISEMENT
Ana sa ran Tinubu zai dawo Nijeriya mako mai zuwa bayan kammala ibadar Umrah.













