Abubuwan Da Duniya Ke Kara Sani Game Da Kasar Sin A Lokacin “Makon Zinare”
Kafafen yada labarai na duniya, ciki har da Reuters, sun mai da hankali sosai kan lokacin hutun bikin ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin da aka kammala kwanan nan. “Duk duniya ta san cewa Sinawa suna hutu” ya shahara sosai a yanar gizo. A lokacin hutu na kwanaki bakwai, yawan zirga-zirgar fasinjoji da aka yi jigilarsu a sassan yankuna daban daban na Sin ya kai biliyan 2.142, kana matsakaicin yawan fasinjojin a kowace rana ya kai miliyan 306, wanda ya karu da kashi 0.6 cikin dari bisa makamancin lokacin bara. “Makon Zinare” lokaci ne da al’umma suka kashe kudi wajen sayan kayayykin bukata, wanda hakan ya baiwa kasar Sin karin damar samun kudaden shiga. Shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 ya fadada bukatar cikin gida a matsayin ginshiki mai muhimmanci, yana mai da hankali sosai kan inganta kashe kudi. Daga ranar 1 zuwa ranar 6 ga watan Oktoba, zirga-zirgar masu sayayya da yawan kudaden shiga a cibiyoyin kasuwanci 78 da ma’aikatar kasuwanci ta sa ido a kansu sun karu da kashi 2.5% da kashi 4.7% bi da bi bisa makamancin lokaci na bara. Hutun ya kuma nuna jajircewar Sin na bude kofa ga duniya. Masu yawon bude ido na Sin sun yi tafiya zuwa birane sama da 2000 a duk duniya, wanda hakan ya haifar da karuwar kudaden shiga ga harkokin sufurin jiragen sama, masaukai, cin abinci, da kuma harkokin kasuwanci na kasashen waje. A sa’i daya kuma, adadin masu yawon bude ido da suka shigo Sin a lokacin bikin tsakiyar kaka da kuma na ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin ya samu karuwa sosai, inda yawancin masu yawon bude ido na kasashen waje suka bayyana cewa tafiye-tafiyensu zuwa Sin abin ban mamaki ne da ba za a manta da shi ba. Yayin da ake aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15, karfin sayayya na Sinawa zai kara habaka, wanda hakan zai kara zurfafa huldar Sin da sauran kasashen duniya. (Safiyah Ma)



















